Gaskiyar Labarin Makancewar Jaruma Shehu Hassan Kano ?~ Shehu Hassan Kano
Fitacce jarumi, kana kuma jigo a masana’antar (Kannywood) Alhaji Shehu Hassan Kano, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewar wai “ya makance ba ya ganin komai da idanuwansa”.
Shehu Hassan Kano ya musanta labarin makancewar tasa ne a ya yin zantawarsa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta wayar salula a wannan rana.
Shehu Hassan Kano ya kuma ƙara da cewa a kwanakin baya ya yi rashin lafiya wacce ta kai ga an yi masa aikin ido, ba wai makancewa ya yi ba, kuma ko a yanzu haka ya na ganin komai rangaɗaɗau da idanuwansa har ma ya na iya gani da karanta rubutu ba matsala.
A ƴan kwanakin da su ka wuce an yi ta yaɗa jita-jitar cewa Shehu Hassan ɗin idanuwansa sun samu matsala har ma ba ya iya gani da su, ya yin da a wannan rana ya tabbatarwa da jaridar Dokin Ƙarfe TV cewa wancan labarin ba gaskiya ba ne ya na gani.
Allah yayimana jagora akan abunda mukasa agaba
Inayimaku fatan alkairi agareku masoya annabi saw
Allah ya kyauta ya karemu daga sharrin xamani