Bidiyo : kalli Yadda Dr Ahmad Gumi ya tubar da yan bindiga Da Masu Garkuwa Samu Da Dubu Suka Ajiye Makamai


Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi jiya talata tare da jama’arsa sun shiga jejin Kidandan-Dajin wanda ya hada da jejin Giwa da Birnin Gwari domin isar da da’awar Musulunci ga fulanin jeji da masu garkuwa da mutane
Wannan shiga jejin da yayi tazo da babbar nasara, domin manyan Kwamandojin masu garkuwa da mutane guda goma da mayakansu sama da dubu daya sun ajiye makamai
Mujahidin Malamin ya kuma jagoranci assasa ginawa fulanin jejin Asibiti da Makaranta da wurin koyon sana’a, domin bai yiwuwa ka raba mutum da ta’addanci ba tare da ka bashi sana’a ba
Cikin tawagar Dr Ahmad Gumi akwai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna CP UM Muri da tawagarsa
Alherin Allah Ya kai ga Dr Ahmad Gumi, jama’a ku shaida daga yanzu har abada Dr Ahmad Gumi ya zama namu, abinda yakeyi na kokarin magance matsalar garkuwa da mutane bataliyar sojoji da ‘yan sanda dubu ba zasu iya ba, gwamnatin Kaduna ma ba zata iya ba don abin yafi karfinta
Ya kamata Gwamnatin Nigeria ta tallafawa Dr Ahmad Gumi da duk abinda ya kamata, domin ya dauko hanyar magance matsalar fulanin jeji masu garkuwa da mutane wanda idan gwamnatin Nigeria zata kashe kudi biliyon dari ba zata samu yadda take so ba
Kuma idan zai yiwu, ya kamata Dr Ahmad Gumi ya kafa wata babbar gidauniya wanda gwamnoni na jihohi da na tarayya da na kasashen waje da mu jama’ar Nigeria za’a tallafa da kudi da kayan sana’a wanda za’a taimaki fulanin jejin da aka rabasu da dabi’ar garkuwa da mutane
Muna rokon Allah Ya kara wa rayuwar Dr Ahmad Gumi albarka, Allah Ya daukaka darajarsa, Allah Ya cika masa burinsa, Allah Ya tsareshi daga dukkan sharri da abin cutarwa Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
Ga bidiyon nan kasa.