Labarai
Barin Masallatai da coci-coci su ci gaba da Ibada da Bude kasuwanni da Makarantu ne yasa Coronavirus/COVID-19 ta dawo~ Boss Mustapha
Sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma shine shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19, PTF ya bayyana cewa sake bude gari ne ya dawo da cutar Coronavirus/COVID-19 a kasarnan.
Kamar yadda hutudole na ruwaito.Ya bayyana hakane a jawabin da sukawa manema labaran, inda yace sake bari a ci gaba da tafiye-tafiye da bude guraren ibada da makarantu da kasuwanni ne yasa Coronavirus/COVID-19 ta dawo..
Yace dolene a dauki matakan kariya dan dakile yaduwar cutar