An Kubutar Da Mutane 104 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Jihar Katsina A cikin (Hotuna)
za mu kubutar da duk wanda ya ke tsare hannun ‘yan bindigar sun sako su ta bin wannan hanyar
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Kimanin mutane dari da hudu, mafi yawancin su mata da kananan yara da yan bindiga suka sace a wasu kauyukan kananan hukumomi jihar Katsina, da ke fama da matsalar tsaro, ba tare da biyan kudin fansa ba kamar yadda gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan.
Gwamna Masari ya bayyana haka ne, a gidan gwamnati jihar Katsina, a lokacin da jami’an tsaro suka hannanta, wadanda aka kubuton daga hannun ‘yan bindiga ga gwamna Aminu Bello Masari.
Masari ya kara da cewa hanyar da muka bi, muka kubutar da daliban makarantar sakandire ta Kankara,su dari ukku da arba’in da hudu ita muke amfani da ita don ganin an kubutar da duk wanda suka sata an amso su ba sai ‘yan jihar Katsina ba, ko wace jiha take. Mafi yawan su sun fito daga karamar hukumar Batsari da Danmusa da kuma Jibia, amma yan Batsari sun fi yawa, akwai na karamar hukumar Batagarawa, har da ‘yan jihar Kaduna, mun bada su sun koma jihar Kaduna.