Labarai
Allah Ya yi wa Iyan Zazzau Bashir Aminu rasuwa


Advertisment
Iyalansa ne suka tabbatar wa da BBC labarin mutuwar tasa inda suka ce ya rasu ne a Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.
Iyan Zazzau na daga cikin waɗanda suka nemi sarautar Sarkin Zazzau bayan rasuwar Marigayi Sarki Shehu Idris a watan Satumban 2020.
Marigayin dama yana da ciwon suga kamar yadda iyalansa suka tabbatar.