A Baiwa Masu Maɗigo Da Luwaɗi Ƴancin Yin Abinda Suke So A Najeriya, Inji Aisha Yesufu
Munafukan banza munafukan wofi, sai ku zo bainar jama’a kuna zagin wasu smma a ɓoye kuna luwaɗi, A’isha Yesufu ta caccaki ƴan Arewa
A jiya ne dai tauraruwa mai fafutuka, A’isha Yesufu ta nemi a baiwa masu Maɗigo da Luwaɗi ƴancin yin abinda suke so.
Ta bayyana cewa ba tana goyon bayan abinda suke bane amma idan abinda suka zaɓa su yi kenan to a basu ƴancin yin hakan.
Wadannan kalamai nata sun jawo cece-kuce sosai inda akai ta Allah wadai da ita, musamman daga Arewa.
Saidai a nata martanin, A’isha ta bayyana ƴan Arewa a matsayin munafukai wanda tace suna zuwa a bainar jama’a suna sukar wasu amma a boye suna Luwaɗi.
Tace uba zaiwa ɗiyarsa fyaɗe ko kuma matar aure ta fita waje tana yawon banza amma sai ace a rufa asiri. Tace ana zagin matan Edo da cewa suna zuwa ƙasar Italiya suna Karuwanci amma suma ƴan Arewa sun manta da ƴan uwansu dake zuwa ƙasar Saudiyya suna yawon karuwancin maza da mata.
Ta bayyana cewa a Sabon Gari dake Kano, Akwai maza da mata dake Karuwanci sannan akwai masu zuwa Islamiya da makarantar kwana ta yara suna daukar su suna luwaɗi dasu.
A’isha ta bayyana cewa addinin Musulunci ba gadon kowa ba ne, addini ne na Ilimi, wasu basu da ilmin Boko dana Arabi amma suna nan suna caccakar wasu.
-Majiya Idon Mikiya
Tir da irin wannan jahilcin tunani