YANZU-YANZU | Abdulraseed Maina Ya Yanke Jiki Ya Faɗi A Kotu
Tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na Najeriya Abdulrasheed Maina, ya yanke jiki ya faɗi yanzu a daidai lokacin da lauyan sa, Anayo Adibe ke gabatar da ƙara a gaban mai shari’a Okon Abang da ke jagorantar shari’arsa.
Kafin faduwar Maina, lauyan nasa yana gabatar da roƙo ga kotu ne, inda ya nemi kotun ta ɗage sauraron shari’ar domin samun damar gabatar da karar ya kuma shirya don shigar da karar da yake niyyar gabatarwa a madadin wanda yake karewa.
Kamar yadda majiyarmu ta samu daga shafin dokin karfe.Ba tare da bata lokaci ba kotu ta tashi tsaye don baiwa jami’an hukumar gidan yari da kuma waɗanda ke da alaƙa da Maina damar kulawa da yanayin da yake ciki.
Daga lokacin da Maina ya faɗi zuwa gama tattara wannan rahoto babu wani labarin dake cewa ya farfaɗo, ko ya fara samun kansa.
Maina, wanda Hukumar EFCC ke tuhumar sa da laifuka 12 na almundahanar kuɗaɗe da adadinsu ya kai naira biliyan N2bn, ya karya ƙa’idojin belin sa, wanda ya tilasta alƙalin kotun, Mai Shari’a Abang Okon, ya bayar da sammacin kamo shi.
-Idon Mikiya