Labarai

Yanzu Na samu kudi zanje a Canja Min Al’aurata zuwa ta Mata ~ Bobrisky

Na kammala Digiri babu aikin yi shiyasa na koma shigar mata, yanzu na samu kudi zanje a Canja Min Al’aurata zuwa ta Mata ~ Bobrisky

Tauraron me shigar mata, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya bayyana cewa dalilin da yasa shi ya koma shigar mata shine ya kammala Karatun jami’a amma babu aikin yi.
 
 
Yace yana dan shekaru 25 ya kammala karatun jami’a amma bai samu aikin yi ba, yace amma yaga abokansa mata sai samun kudi suke suna haskakawa.
Kamar yadda Hutudole na ruwaito, yace shi kadai ya koma yayi Nazarin me ya kamata yayi, yace da farko yayi tunanin fashi da makami amma yaga bashi da zuciyar kwacewa mutane kudinsu, yace daga baya shine yayi tunanin fara shigar mata, yace shekara daya da fara shigar mata kawai sai yaga ya daukaka kuma ya samu kudi sosai.
 
 
Yace abin ya matukar bashi mamaki dan haka sai ya kara bada himma. Yace a yanzu kam yana kudi iya kudi kumama ya tara dala 300,000 zai je a canja masa al’aurarsa ta koma ta mata, ya zama cikakkiyar mace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button