Kannywood

WATA SABUWA| Rayuwata Tana Cikin Hadari Matukar Ban Hadu Da Hafsat Idris Barauniya ba~Inji Matashi Ahmad Umar

Wani matashi dan asalin jahar Sokoto mai suna Ahmad Umar Namadina ya bayyana cewa rayuwarsa tana cikin hadari matukar bai hadu da jaruma Hafsat Idris Barauniya ba.
Ahmad ya bayyana cewa hatta abinci bai iya ci har sai an rarrashe shi saboda tsanin soyayya da tunanin jaruma Hafsat Idris.
Ahmad ya ce yayi kokarin zuwa Kano wajen jarumar amman sai aka gaya masa cewa hanyoyi basuda kyau saboda matsalar tsaro da yawan hadurra da akeyi.
Akan haka Ahmad ya roki jaruma Hafsat Idris data taimaka ta shigo jirgi tazo Sokoto domin su hadu, ko kuma jarumar ta tura masa da kudin jirgi ya je can Kano su hadu.
Amman matashin ya ce rashin haduwa da jaruma Hafsat Idris na iya jafe rayuwarsa cikin hadari.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga kafa sada zumunta a facebook mai suna “Nasara”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button