Addini

Tsadajjiyar Nasiha Daga Tekun Ilmi Sheikh Dr Muhammad Sani Umar rijiyar lemo

Rashin tsaro ko tabarbarewar tattalin arziki ko ci bayan al’ummah, mu a wajenmu Musulmi mun san cewa yana da sababi wanda Allah Madaukakin Sarki ya sanya hakan a matsayin sunnar Sa, sunnar Allah ba zata canza ba, kamar yadda Allah Ya fadi hakan a Qur’ani
Yana daga cikin sunnonin Allah idan rashin gaskiya da sabon Allah a tsakanin bayinSa ya yi yawa, to Allah Zai iya saukar da masifar da ba zata ware wani ba, idan tazo zata shafi kowa da kowa
Idan muka dubi rayuwarmu zamu ga zalunci yayi yawa, abubuwan da suke faruwa na zalunci daga sama har kasa shi yafi yawa, har ma ya zama wani salo na rayuwa, wanda bai iya zalunciba ba zai ji dadin rayuwarsa ba
Zalunci da rashin gaskiya ya wanzu a tsakaninmu daga mataki na shugabanni zuwa na talakawa da masu wadata, maza da mata, babba da yaro kowa yana tunanin hanyar da zai zalunci ‘dan uwansa
Idan ya zamto wannan itace rayuwarmu to Allah ba Zai barmu mu zauna lafiya ba, idan zaluni yayi yawa Allah ba Ya kyale gari a zauna lafiya, Zai yi kaca-kaca da shi
Hakanan idan fasikanci aka daure masa gindi, ya zamto manya daga gurinsu ake kwaikwayon fasikanci, to wannan itama alamace na cewa Allah Zai kacaccala wannan garin, ana aikata salon fasikanci iri-iri wanda da can ba’a san su ba, kuma ana daure musu gindi
Canj, ba canjin shugaba shine canji ba, idan zamu canza shugabanni dari amma bamu canza halayenmuba ba zamu taba ganin canji ba, wannan kuma fadar Allah ce
Shekaru shida da suka wuce ba canji muke nema ba? anzo anyi canjin shugabanci abubuwa suka dawo suka dada cabewa, kuma muka sake cewa canji, kuna zaton don anyi ta canza shugabannin amma mu a dabi’armu a halayenmu alakarmu da Ubangiji bata canza ba shikenan sai Allah Ya canza mana?, sunnar Ubangiji ce wannan, Allah ba Ya canzawa mutane sai sun canza kansu
Allah Ya jikan wani Malami da yake wata magana da ta zama tamkar wata gwal, yake cewa ku kafa Daular Musulunci a karan kanku sai ku ga ta kafu a Kasarku, idan kuka gyara kawunanku sai kuga shugabancinku ya gyaru
Duk wata ni’imar da mutane suke ciki ta zaman lafiya ko ta tattalin arziki ko ta cigaba Allah baya canza ta sai idan mutanen ne suka canza, idan alakarmu da Allah tayi kyau duk wannan koke-koken ba zamu yi shi ba. ~Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Allah Ka bamu ikon tuba, Ka tausaya mana, Ka kawo mana karsheb fitina da tashin hankali a Kasarmu Nigeria
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
A KULA:
Ina son in kara tunatar da mu cewa, bayan tuba akwai bukatar mu yawaita sadaka ga mabukata wadanda suke birjik a ko ina a cikin kasarmu. Sadaka maganin musibu ce.
Wallahul musta’an.majiyarmu ta samu daga shafin Dr mansur sokoto

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button