To Fah ! Auren Mai Mata Yafi Komai Dadi A Duniya ~ inji Wata shantalelliyar Budurwa
Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @IlhamSafiyyat ta bayyana cewa auren namiji mai mata shine zabi mafi kyau saboda abubuwa da dama da ke tattare da hakan.
@IlhamSaffiyat ta bayyana cewa irin wannan aure na zuwa da garabasa; ga miji sannan ga yar’uwa.
Yar’uwa da take nufi a nan shine matar da sabuwar amaryar za ta je ta tarar a gidan mijin.
Yayinda wasu suka caccaketa akai, wasu yan tsiraru sun yarda da shawararta.
Ga abinda wannan budurwa ta wallafa a shafin ta na sada zumunta.
Getting married to a married man is the best thing because it comes with a bonus a husband and a sister❤️
— MAR’ATUSSALIHA??❤️ (@IlhamSafiyyat) December 13, 2020
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
@Sir_Babex ya ce:
“Allah ya yi maki albarka a kan wannan fahimta taki. Ki ji ma, idan Allah ya yarda sai kin auri mai mata uku, domin ki samu tarin garabasa.”
@khalidGabary ya ce:
“Kawai ki fada mana cewa da mai aure kike soyayya.”
@Obasteve91 ya ce:
“Ba a kasar Yarbawa ba. Za ki shirya wa kanki da yaranki da basu ji ba basu gani ba gadar kiyayya.”
@Nasir1on1 ya ce:
“Bugu da kari za ki zama mata ta lokaci zuwa lokaci: Kwana biyu da miji sannan kwana biyu babu miji. Wani dadi ke cikin haka!”
@KabiruIyayi ya ce:
“Kin yi gaskiya, ci gaba biyu kenan.”