Addini

Sheikh Bala Lau, Ya Bada Umurni Ga Limamai Da Su Dukufa Da Addu’oin Al-qunut A Fadin Kasa

Sheikh Bala Lau, Ya Bada Umurni Ga Limamai Da Su Dukufa Da Addu’oin Al-qunut A Fadin Kasa, Don samun taimakon allah kan kalubalen tsaro
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar Ahlussunah JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce komawa ga Allah da yawan istigfari ne hanyar samun saukin kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan Najeriya musamman arewa maso gabar da arewa maso yamma.
A sanarwa daga ofishin shugaban da ke umurtar limamai na dukkan masallatan kungiyar su shiga jagorantar addu’o’in alkunut don taimakon Allah, ya ce rike gaskiya da amana za su karfafa karbar addu’o’in jama’a.
 
 
Shehun malamin ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da jami’an tsaro su yi tsayin daka kan kare rayuka, mutunci da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
 
 
A nan shugaban na JiBWIS ya jaddada ta’aziyya ga wadanda ‘yan Boko Haram su ka hallaka a arewa maso gabar da buga misali da wadanda a ka yanka a Zabarmari, kazalika ya jajantawa iyayen ‘yan makarantar sakadandaren Kankara a Katsina da ‘yan bindiga su ka sace ‘ya’yan su, ya na mai addu’ar samun kubutar yaran cikin salama.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button