Labarai

Satar dalibai a Kankara, cin fuska ne ga shugaba Buhari~ Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Advertisment

 
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya jagoranci Jama’atu Nasril Islam (JNI), ya bayyana sace daruruwan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS), daliban Kankara, a matsayin sara a fuskar Shugaba Muhammadu Buhari.
 
Kungiyar koli ta Musulunci a Arewa ta ce, karfin gwiwar da ‘yan bindiga suka yi na satar a ranar da Shugaban kasa ya isa Jihar Katsina a wata ziyarar da yakai, ya nuna cewa akwai bukatar Gwamnatin sa tayi da gaske don magance matsalar tsaro.
 
Majiyarmu ta samu daga hutudole,a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Litinin ta hannun Sakatare-janar, Dr. Khalid Abubakar Aliyu, JNI ya bayyana karara cewa, akwai gurguzu a cikin tsarin tsaron Najeriya da ke bukatar a hanzarta kuma a magance su da sauri.
 
Amma ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya saurari kiraye-kiraye daga ‘yan Najeriya na sauya fasalin harkar tsaro da kuma yi wa kasa jawabi, inda ta kara da cewa, akwai maganganun da ke nuna cewa don samun kudi, wasu manyan jami’an tsaro ba sa so a kawo karshen rashin tsaro.
 

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button