MU SHIRYA MUTUWA: Cutar Da Za Ta Ci Duniya Na Shirin Ɓulla – Hukumar Lafiya
Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta yi gargaɗi ga duniya baki daya da a shiryawa bullar wata ƙwayar cutar da ta fi COVID-19 hatsarin gaske da ka iya kawar da duniya baki daya.
Shugaban hukumar ɓangaren shirye-shiryen agajin gaggawa, Dr Mike Ryan ya bayyana haka ranar Laraba yana mai cewa COVID-19 mummunar cuta ce, amma akwai wacce ta fi ta, kuma tana nan zuwa.
A cewar ta bakin Dr Ryan, lokacin da yake ganawa da yan jarida ya ce corona “Kawai mai sharar fage ce amma wannan ta fita.
Mu na koyon yadda za mu yi abubuwan ne da kyau, kimiyya, rarraba kayayyaki, horaswa da sadarwa su zama sun inganta. Amma gaskiya duniyar nan bata da tabbas.
“Muna rayuwa cikin zamantakewa iri-iri. Wannan barazana za ta cigaba. Idan akwai abu daya da za mu koya daga wannan annobar, shine aiki tare. Yana da kyau kuma mu karrama waɗanda muka rasa ta sanadiyar yaƙi da wannan annobar”.
Dr Ryan ya ƙara da cewa “Wannan annobar ba ƙaramar masifa ba ce, ta girgiza kowanne ɓangare na duniya. Amma ku sani, wannan ba ita ce babbar annobar ba.”
Cutar korona dai ta kama sama da mutan miliyan 82.6 a faɗin duniya inda sama da mutum miliyan 1.8 suka riga mu gidan gaskiya tare da kassara tattalin arzikin duniya.
A yanzu haka dai ana rarraba miliyoyin magungunan riga-kafin wannan cutar da aka yi nasarar samu wanda hukumar lafiya kuma ta amince da ingancinsu.
Ya kuke kallon wannan Furuci?