Labarai

Mata Da Ake Zargin Ta Kashe Ƴaƴanta A Kano Ta Gurfana A Kotu

Kotun majistare mai lanba 5 ƙarƙashin mai shari’a Hauwa Lawan Minjibir, itace wadda aka gurfanar da Hauwa Habib mazauniyar unguwar Ciranci dake birnin Kano, inda ake zargin ta da kashe ƴaƴanta guda 2 da kuma yiwa wata yarinya rauni.
Tun a watan goma na wannan shekarar ne aka sami wannan matar da wannan ɗanyan aiki.
Lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Ɗinki, shine ya gabatar da ita aka kuma karanta mata tuhumar da ake mata amma ta musanta.
Nan take Lauyar da take kareta wato Barista Huwaila Muhammad Ibrahim, ta buƙaci kotu da ta amince akai matar asibiti domin duba ƙwaƙwalwarta, sai dai Lauyan gwamnati baiyi suka ba, inda nan take kotu ta amince.
Yanzu haka dai an ɗage zaman zuwa 5 ga watan Janairu 2021.majiyarmu ta samu daga shafin dokin karfe

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button