Jagororin Rusa Arewacin Nigeria Waɗannan Su Ne ~ Dr Ibrahim Jalo Jalingo
Wanda ya rubuta Ash-sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo
1. Murakkaban Jahilan Barebarinmu masu ta’addancin bokoharam, da kuma Jahilan Fulaninmu masu ta’addancin fashi da makami da kidnapping. Lalle wadannan gurbatattu cikin wadannan kabilu biyu namu sun yi matukar kunyata mu mu da muke Barebari da Fulani. Lalle sun yi matukar kunyata mu a idanun makiyanmu na cikin gida da waje. Lalle sun yi matukar kunyata mu a idanun al’ummar Duniya.
2. Gurbatattu mara kishin kasa cikin jami’an tsaronmu, musamman cikin ‘Yan sandanmu da Sojojinmu wadanda tsarin mulkin Kasa ya dora musu alhakin tsaron Kasa da tsaron ‘Yan Kasa, amma abin bakin ciki da takaici suka koma suna ta aikin karya dokar Kasa, suka durkushe suka yi baya suka sanya rigar ragwanci da lalaci, suka daina yakar ‘yan ta’adda da bata gari, suka daina shiga dazuka da tsaunuka da lunguna domin zakulo ‘yan ta’adda da bata gari ‘yan kidnapping a mabuyarsu, suka koma babu abin da suka fi yawan yi sai kwace wa talakawan Kasa miskinai ‘yan kudadensu a manyan hanyoyin da ke cikin wannan Kasa tamu. Yaa Lal Lallah, Wa Yaa Lal Ajab!!
3. Gurbatattun ‘Yan siyasa wadanda suka fadi zabe tare da ‘yan bangarsu na siyasa da ‘yan maulansu wadanda suka mayar da kawunansu tamkar kakaki, tamkar ‘yan bangar ‘yan ta’adda da ‘yan kidnapping; saboda kawai gigitar faduwar zabe, saboda kawai zafaffar hamayyarsu da kiyayyarsu ga abokan hamayyarsu wadanda suke a kan karagar mulkin Kasa.
4. Gurbatattun jami’an Gwamnati mara kishin kasarsu, mara kishin wadanda suka nada su a kan mukamansu, wadanda babu abin da ya dame su in banda cika aljihunsu da kudaden haram, amma ba wai gina Kasa da gina al’ummarta ba da kuma kawo mata ci gaba ta ko wane bangare ba!!
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tausaya mana Ya cusa wa wadannan nau’ukan mutane kishin kasarsu da kishin al’ummarsu ta yadda za su koma su zamanto mutanen kwarai, ‘yan Kasa na kwarai, masu aikin gina kasarsu da al’ummarsu.
Lalle mu ‘yan Arewa ne kadai za mu gina arewarmu. Lalle mu ‘yan Nigeria ne kadai za mu gina Nigeriyarmu, amma ba wai Mala’iku ne za su sauko daga sama ba domin gina mana!! Allah Ya taimake mu.