Kannywood
Ina Son Kirsimeti, in kun ga dama kuce ni ba musulma bace dadin Abin Musulunci ba gadon gidanku bane~ Mansurah Isah
Bayan caccakar da akawa tauraron dan kwallon kasar Egypt, Mohamed Salah kan yin murnar ranar Kirsimeti, Tohuqar Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta goyi bayansa.
Salah ya saka hotunansa tare da iylansa sanye da kayan murnar kirsimeti, saidai wasu musulmai da dama sun caccakeshi akan hakan da cewa bai dace ba.
View this post on Instagram
Mansurah Isah ta saka Hoton Mohamed Salah a shafinsa inda ta bayyana cewa tana son Kirsimeti sannan kuma tana cin kaza a ranar Kirsimeti.
Hutudole nayi kokarin tattara bayanai tace tana da iyalai da abokai da take yin murnar kirsimetin tare dasu. Tace idan kun ga dama ku ce ni ba musulma bace amma Musulunci gadon gidan ku bane, Allah(SWT) na kowane .
Ga kadan daga cikin musanyar baki da tayi da wasu.
Man tashabbAha bi qaumin fahuwa minhum