Idan Ɓera Da Sata !!An Fara Taya Maryam Ab Yola Murnar Zata Koma Gidan Adam A Zango
Jarumi Adam Ya Zango yayi wata al’mara bayan daya sanya hoton tsohuwar matarsa Maryam Ab Yola Inda ya rubuta cewa kowa ya fadi raayinsa.
Ko da wallafa wannan hoton sai tsohuwar jarumar tazo tayi alamun kunya wanda nan take aka fara bayyana raayoyi inda maka akasari wasu ke rokon jarumin daya maida dakinta.
View this post on Instagram
arewamobile ta kara da cewa wasu kuma har sun fara tayata murna ungulu zata koma gidanta na tsamiya inda yan kalilan ne kawai basuyi mata fatan komawa gidan tsohon mijinnata ba.
Idan baku manta ba mun taba kawo maku wata hira da akayi da amaryar Adam A Zangon inda ta nuna ita fa sam bata kishi da Maryam Ab Yola hasalima ita tana shaawar kallon finafinanta.
Wannan abu dai kam yayi ma Maryam Yola dadi inda tayi ta sanya raayoyin da mutane bayyana a story dinta na Instagram.
Tun bayan dai rabuwar Adam A Zango da Maryam Ab Yola alaka batayi tsami ba wanda ko bayan dawowarta masanaantar kannywood jarumin ya sata a fim dinsa mai suna Ramakon Gayya kuma lokaci zuwa lokaci sukan taya juna murnar Birthday.
Ina fatan nasara a rayuwa a koda yaushe Allah ya kara albarka ya kara hazaka da ci gaba irnna alkhairi