Kannywood

Harkar fim za ta iya kai mutum Aljanna ko Wuta ~ Yusuf Sasen ” Lukman A Labarina”

YUSUF Muhammad Abdullahi (Sasen) ya na ɗaya daga cikin jarumai masu tasowa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood. Jarumi ne a cikin shirin nan mai dogon zango na ‘Labari Na’ wanda tashar talbijin ta Arewa24 ke haskawa, inda ya fito a matsayin Lukman.
A hirar sa da mujallar Fim, Sasen ya bayyana cewa ‘Labari Na’ ba shi ne shirin sa na farko ba amma dai shi ne silar ɗaukakar sa a duniya wanda kuma kan sanya shi farin ciki a ran sa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: Ya aka yi ka samu kan ka a cikin shirin ‘Labari Na’?
SASEN: Shirin ‘Labari Na’ da na tsinci kai na a ciki ya faro ne daga wani furodusa mai suna Sani Mai Iyali a lokacin da mu ke yin wani shiri mai su na ‘Camfi’. Sannan zan ma iya cewa Malam Aminu Saira ya taɓa yi min tayin fim ɗin ‘Labari Na’ kuma kamar yadda na ke faɗe shi Malam Aminu Saira mutum ne wanda ya san inda mutum ya dace ya fito a fim, sannan shi Sani Mai Iyali ya ke gaya min cewa an fa ware min guri na a cikin wannan shirin kuma an san zan doke kowa a gurin. Na ce a’a, babu matsala. Daga nan kuma na samu kira daga shi Malam Aminu Saira, ya gaya min lokacin da ya dace na zo domin fara ɗaukar fim ɗin ‘Labari Na’.
FIM: Ya ka ji lokacin da aka fara ɗaukar ‘Labari Na’?
SASEN: Ka san farkon fara fim yadda yanayin mutum ya ke, musamman ni da na taso daga gidan kunya kuma ina da kunya, dole za ka ji ba ka saba ba, in aka sa ma kyamarar da kwarjini; sannan mutum zai ji ya ɗan firgita kawai kuma ka razana.
FIM: Yaya mu’amalar ka ta koma lokacin da aka fara haska shirin idan an dubi yadda ya ɗau lokaci a ajiye? Mai yiwuwa ma ka manta ka yi wani fim mai suna ‘Labari Na’!
SASEN: Abin ya ba ni mamaki saboda ka san mu mun riga mun yi fim ‘Labari Na’ amma an daɗe da yin shi. Kuma abin da ya ke ba ni mamaki shi ne duk inda na je sai in ji ana kira na, “Lukman Lukman”. Wani lokacin ma ni ba na juyawa sai dai in na ji kiran ya yi yawa har mutane su fara cewa ana yi ma magana ko kuma su tsaya a gaba na. Sai na ce lallai ‘Labari Na’ ya yi tsawo kenan, ya je wuraren da ban taɓa tsammanin zai je ba.
Kuma in na ga hakan, ya kan sa ni farin ciki. Ba zan iya misalta yadda na ke ji ba, sai dai kawai in ce alhamdu lillah. Kuma ba wani abin daɗi illa a ce mutane su na ƙaunar ka kuma su na son ka. Wannan gaskiya babbar nasara ce a duk abin da ake a rayuwa a ce mutane sun karɓe ka, don masu iya magana su na cewa shaidar duniya ita ce ta ƙiyama kuma jama’ar nan su ne mutanen duniya gaskiya.
FIM: Wane matsayi ka ke takawa a cikin shirin ‘Labari Na’?
SASEN: Ina taka rawa a cikin shirin a matsayin Lukman. Lukman shi mutum ne mai hankali, mai sanin ya-kamata, mai tausayi kuma da hangen nesa, wanda ya yarda cewa ɗan’adam ya na da daraja, kuma ba yadda za a yi ka yi amfani da matsayin ka ka danne wa wani haƙƙin sa. A taƙaice, Lukman cikakken mutum ne.
FIM: Shin ko ‘Labari Na’ shi ne fim ɗin ka na farko?

Yusuf Sasen tare da su Abba El-Mustapha a lokacin ɗaukar wani fim

SASEN: Shirin ‘Labari Na’ shi ne aikin fim ɗi na na uku. Akwai wani fim da mu ka yi na marubuci Ibrahim Birniwa mai suna ‘Ciki Da Magana’, shi ne fim ɗi na na farko, amma na fito ne a matsayin mai taimaka wa jarumi, don ko magana ma ban yi ba a fim ɗin. Fim na biyu kuma shi ne na mawaƙi Nazifi Asnanic mai suna ‘Camfi’, sai kuma ‘Labari Na’ wanda kuma a cikin shi aka san ni ko ma na yi suna sosai.
FIM: Bayan fitar ‘Labari Na’, ka samu kiraye-kiraye daga cikin furodusoshi?
SASEN:
Na samu kira da dama daga manyan furodusoshi irin su Abdul Amart Maikwashewa a cikin fim ɗin sa mai dogon zango na ‘Manyan Mata’. Akwai kuma wanda na yi da Kwakwatawa wanda a ciki aka ba ni cikakken jarumi, sunan fim ɗin ‘Saura Ƙiris’, da kuma wani fim da na ke yi a yanzu mai suna ‘Sirrin Ɓoye”. Akawai dai finafinai da dama da na ke yi a yanzu waɗanda wasu ba za su faɗu ba. Kuma ina godiya da irin damarmakin da aka ba ni.
FIM: A ƙarshe, menene kiran ka ga abokan aikin ka masu tasowa?
SASEN: Kira na shi ne don Allah don Annabi tunda gaɓa ta zo ta fim ɗin nan kuma ana yin sa kuma ko ina a duniya yawanci ana yin fim, to amma akwai lokacin da za ka gani mu ‘yan fim ɗin mu ne waɗada su ka fita daga layi na gaskiya da daidai. Akwai lokacin kuma idan mutane su ka yi amfani da yawun su su ka aibata mu a daidai lokacin harkar ce za ta lalace mana gaba ɗaya, kuma idan ‘yan fim su ka lalace ga baki ɗaya ko kuma ɗa na wani ya lalace to lallai wanda su ke tare da su su ma zai iya lalata su. Abin dai na ke nufi cewa idan mutane su ka hangi cewa ɗan fim ko kuma ni ko wasu sun yi ba daidai ba, don Allah don Annabi in da hali su kirawo su su yi masu nasiha. Idan ba su kirawo su ba ko kuma sun mAsu nisa, to don Allah ku yi masu addu’a Allah Ubangiji ya dawo da mu daidai mu kuma mu yi abu na daidai. Don a yanzu ko wanne addini su na anfani da fim don nuna al’adun su.
Kuma maza da matan mu na cikin masana’antar Kannywood su sani cewa wannan abin da Allah ya ba mu mu ɗauke shi cewa addini ne, saboda sana’a kamar yadda mutum ya ke aikin soja ko kuma ɗan kasuwa zai tafi mu ma mu tabbatar cewa haka mu ka fito neman abinci. Kuma mu sani cewa duk motsin da mutum zai yi addinin sa ya ke wakilta. Idan ka na da abu da ya shafi rayuwar sa ya tsaya iya kan ka amma ka tabbatar cewa al’umma ka ke wakilta, kuma ka zama wani gwarzo da al’umma su ke kwaikwaya. Kazalika idan ka yi abu mai kyau mutane da yawa za su kwaikwaya. Kada mutane su ɗauka kawai “na zo in yi fim ne don in ji daɗi”. Idan kuma ka riga ka shiga harkar fim, to rayuwar ka ta canza, ba wai sauran mutane ne yanzu ba. Sannan a ƙarshe mu sani cewa wannan harkar za ta iya kai mu Aljanna, za ta kuma iya kai mutum Wuta. Allah ya kiyaye. Na gode.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button