Labarai

Gwamnati Ta Hana Wani Fati Da Aka Shirya Yi Tsirara A Kaduna

A Yi Awon Gaba Da Wadanda Suka Shirya
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da samun nasarar hana gundanar da wani casu dare na badala da aka shirya wa matasa maza da mata inda za su bayyana tsirara suyi rawa su, su ci abinci su yi shaye-shaye sannan kuma ayi zinace-zinace domin murnar shiga sabuwar shekara.
Majiyar Zuma Times Hausa ta sheida mana cewa a katin gayyatar zuwa fatin an saka sharadin dole ne mutum ya je tsirara, sannan da kororon roba, kanan kuma aka saka kudin shiga daga Naira 2,000, da VIP 5,000 da kuma VVIP 10,000
Sun rubuta a jikin katin cewa sai mutum ya biya kudinsa sannan za a bayyana masa wajen da za ayi casun amma dai masu shirya taron sun bayyana cewa akwai zafafan mata 50 da za su nishadantar da mahalarta taron sannan dukansu mutum na iya saduwa da su a lokacin taron.
Sai dai shugaban kula da harkokin addinai na jihar Kaduna Sheikh Albani a safiyar yau Litinin ya ce, “cikin Ikon Allah mun samu Ikon hana wannan rashin mutuncin da kama wadanda suka shirya. Mai girma Gwamna Mallam Nasiru El-Rufa’i muna GODIYA.”
Hakanan shima mai taimaka wa Gwamnan Kaduna a fannin yada labarai Abdallah Yunus Abdallah ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Mun godewa Gwamnati bisa hobbasan da ta yi wajen ganin ta hana wannan badala”
Gwamnatin dai ta ce bayan hana casun da ta yi sannan kuma ta kama wadanda suka shirya shi domin hukunta su.
-Zuma Times Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button