Labarai

Garba Shehu ya nemi afuwa kan cewa ɗalibai 10 aka sace

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya nemi ga afuwa kan bayanin da ya bayar cewa ɗalibai 10 ne kawai aka sace a makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina kamar yadda bbchausa na ruwaito
“Ina neman afuwa kan kuskuren bayanai da aka gabatar cewa dalibai 10 ne aka sace a makarantar kimiya ta Kankara.
“Wani ne wanda ya kamata ace ya sani ya bayar da bayanan kan adadin ɗaliban. Adadin kuma yanzu ya ci karo da waɗanda aka gani.
“Don Allah a fahimci cewa bayanan ba an bayar da su ba ne domin rage muhimmancin yanayin da aka shiga,” in ji Garba Shehu

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button