Labarai

Da Dumi Duminsa: Wasu yan bindiga sun daddatsa magidanci a Kano

Advertisment

Mutane da ba’a san ko su waye ba, sun kutsa gidan wani mutum mai suna Abubakar Idris mai shekaru 65 a duniya da ke unguwar Kurna tare da daddatsashi da Adda har sai da ya rasu.
 
 
Lamarin dai ya faru ne a daren jiya. dan’uwan mamacin mai suna Dahiru Goma ya shaidawa Freedom Radio cewa mutanen ba su dauki komai a gidan ba, ya kuma ce jim kadan bayan kisan na sa ne suka garzaya da shi Asibiti amma kafin su kai rai yayi halinsa.
 
Dahiru ya kara da cewa “Suna shigowa gidan suka tarar da shi yayi alwala kafin ya tayar da sallah suka hau sassara shi, sun yi masa gunduwa gunduwa sun yi masa rauni ba adadi munje kwamis suka ce sai dai mu ta fi asibitin Murtala, mun ta fi amma kafin mu kai asibitin rai yayi halinsa”
Duk kokarin jin ta bakin hukumar Yansanda akan batun hakan ya ci tura.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button