DA ƊUMI-ƊUMI: Matasa sun kai harin ramukon gayya, sun kashe mata da yara 6 a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutane shida, ciki har da wata mata da yara ƙanana a wani harin ramuwar gayya a karamar hukumar Kauru, biyo bayan harin Zangon Kataf a ranar Alhamis.
A daren ranar Alhamis wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf, inda suka kashe mutane bakwai.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce sojojin rundinar Operation Safe Haven da ‘yan sanda sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna game da hare-haren da ake kaiwa wasu makiyaya a kananan hukumomin Kauru da Lere.
Talla
A cewar Mista Aruwan, yayin da yake bayyana sakamkon binciken jami’an tsaro, ya ce “fusatattun matasa ne suka kai harin, biyo bayan kisan mutane bakwai da aka yi a daren Alhamis a Gora Gan, karamar hukumar Zangon Kataf.
“Jami’an tsaro sun ba da rahoton cewa an kashe makiyaya bakwai a wani kisan gilla a ƙauyukan Ungwan Idi da Kasheku na karamar hukumar Kauru yayin da makiyaya biyu suka samu rauni a ƙauyen Ningi na karamar hukumar Lere”.
Hon. Aruwan ya ce makiyaya bakwai da aka kashe a ƙauyukan Ungwan Idi da Kasheku da ke karamar hukumar Kauru su ne Mustapha Haruna (mai shekara daya), Ya’u Kada (mai shekara ɗaya), Sa’idu Abdullahi (ɗan shekara daya), Zainab Zakari (ƴar shekara ɗaya), Sadiya Abdullahi (ƴar shekara biyar), Aisha Abdullahi (ƴar shekara guda) da kuma wata mata da ta ƙone kurumus ta inda ba za a iya ganeta ba.
Kwamishinan ya ce a halin yanzu akwai mutane biyar da suka bata kuma sojoji na neman su.
Ya kara da cewa, bukkoki shida sun kone a harin.
Mista Aruwan ya ƙara da cewa Aisha Mohammed (ƴar shekaru 20) da Sadiya Abdullahi (mai shekaru 25), wadanda suka samu rauni a harin ramuwar gayya na karamar hukumar Kauru suna karbar kulawar likitoci a ƙaramin asibitin Ungwan Idi.
Kamar yadda hausadailytimes na ruwaito ,ya ce a kauyen Ningi na karamar hukumar Lere, makiyaya biyu, Bingel Odi (mai shekaru 31) da Isa Joda (mai shekara bakwai), sun samu rauni kuma an garzaya da su zuwa Babban Asibitin, Saminaka, a cikin karamar hukumar Lere.
Gwamnan jihar Kaduna ya nuna damuwa tare da yin Allah wadai da harin da aka kai. Ya nemi jami’an tsaro da su tabbatar da kamo duk mai hanu a wannan ta’asa cikin gaggawa.