Kannywood

Buhari ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da korona

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da annobar korona zuwa ƙarshen Maris ɗin 2021

A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba zai yiwu ci gaban da aka samu na watanni tara da suka gabata ya tafi haka nan ba.

Shugaban ya ce “na tsaya na yi nazari kan lamarin kuma na aminta da cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa wajen daƙile yaɗuwar wannan cutar ta korona.

Shugaban ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da kuma malamai da su ba kwamitinsa haɗin kai wurin wayar da kan al’umma kan cutar.

Bbchausa na ruwaito ,a jiya ne dai kwamitin shugaban ƙasar da ke yaƙi da korona ya sake bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

Haka kuma kwamitin ya sanar da rufe duka makarantu da kuma wuraren motsa jiki.

Kwamitin kuma ya saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button