Addini
Bidiyon Ku San Malamanku Tare da Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar
An haifi Dakta Bashir Aliyu Umar a Unguwar Yola a cikin birnin Kano ranar 27 ga watan Yuli 1961.
Ya yi karatun allo har zuwa sauka a makarantar Malam Kabiru Khalil da ke Kofar Ƙwaru cikin gidan Sarkin Kano.
Ya yi karatun ilimin addini da harshen Larabci a wajen malamai da dama a Kano, ciki har da wan mahaifinsa Marigayi Alƙali Idris Ƙuliya, tsohon alƙalin alƙalan Kano kuma tsohon limamin Kano, da Malam Gali na Malam Shamsu na Magangara da Malam Baba na bayan gidan Wazirin Kano da Shehu Muhammadu Barnoma.
View this post on Instagram