Addini

Bidiyo: Qalu innalillahi Wa’inna Illaihirraju’un!! Allah Kuji Wani Irin Cin Amana Daya Faru !!!

Advertisment

Wani gajeren bidiyo na kalla na Sheikh Bin Uthman Kano, yake bada wani labari kamar haka:
Wani mutum ne ya siyar da gidan sa naira miliyan sha biyu (12m), sai aka kawo wa mutumin kudin gidan da daddare, wannan wani makwabcin sa yazo yake ce masa don Allah ya taimaka masa da naira dubu dari biyu (250k), Sakamakon akwai hidima a gaban ta aurar da yarinyar sa ko kuma dai wani abu makamancin hakan kuma bashi da hali. Sai mutumin (wanda ya siyar da gdan) yace ma makwabcin nasa tunda yanzu dare yayi yayi hakuri zuwa da safe sai ya bashi. Suka rabu a haka.
A cikin wannan daren, wannan makwabcin da ya nemi a taimaka masa yaje ya nemo wasu qattin sukazo gidan wannan mutumin da ya siyar da gida. Suka ce masu sunji ya siyar da gidan sa 12m don haka wannan kudin sukazo amsa. Ai kuwa babu wata-wata ya basu wannan kud’i duka. Sai ya rokesu alfarmar cewa su taimaka masa da 250k saboda yayi ma wani makwabcin sa alkawari, don haka ita kad’ai ce bukatar shi ga wannan kud’i.
Jin hakan sai shugaban yan fashin ya bude fuskar wannan makwacin (sakamakon fuskokin su a rufe suke), ya tambayi wannan me kud’in cewa; shin wannan ne makwabcin naka da kayi ma alkawarin? Sai yace, eh shine. Nan take kuwa shugaban barayin yasa bindiga ya harbe shi, yana mai cewa masa “amma Kai ba mutumin kirki bane”!
Nan suka mayar masa da kud’in sa 12m suka tafi.
Ga bidiyon nan kasa ku saurara
https://youtu.be/xZmpgZZl650
DARASI:
*Idan Allah ya bama wani dukiya, kada kayi masa hassada, domin tana kaiwa ga halaka.
*Duk wanda yake kokarin sanya ka farin ciki, kada kaci amanar sa.
*Ka kiyayi hakkin makwabtaka domin ko mugu yana shakkar Makwancin dake kyautata masa.
*Duk wanda zaka taimaka, kayi kokari kayi shi da tsarkin zuciya.
*Ka guji mugun nufi akan yan’uwan ka, domin kuwa idan ya juyo maka bazai maka da kyau ba.
Abu Sufyaan

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button