Addini

Bidiyo : Bayan Ceto Daliban Kankara!! Sheikh Kabiru Gombe Ya Aika Zafaffan sako Akan Gwamnati

A cikin khudubar juma’a da Sheikh Kabiru Gombe ya gabatar a garin Katsina bayan sun gana da shugaba Buhari, Malam yayi wasu maganganu na tsantsar adalci da suka kama hankali sosai
Malam yace: to bari na fada muku, kungiyar IZALA tunda aka kafa Gwamnatin Buhari zuwa yau ba’a dauki mukami ko na mai shara ne an bawa kungiyar IZALA ba
Na rantse da Ubangiji wanda Ya tsaida sama babu ginshiki Gwamnatin nan bata bamu ba, idan kuma wani ya san akwai matsayin da aka bawa kungiyar IZALA ya rufa mana asiri bai fada ba Allah Ya isa ba mu yafe ba duniya da lahira
Ba wai batun bada mukami ga dan kungiyar IZALA ba, shin ba ‘dan darika?, ba dan kadiriyya?, kai har matsiyacin ‘dan shi’ah akwai masu mukami a cikin wannan Gwamnatin..
Abinda nake magana shine a dauki mukami a bawa kungiyar IZALA saboda kokarin da ta yi wajen kafa wannan Gwamnatin nan na rantse da Allah ba’a bamu ba.., inji Sheikh Kabiru Gombe
Abin takaici jama’a, ‘yan shi’ah da suka tsani wannan gwamnatin, suke mata bita da kulli amma wallahi an basu mukamin Minista har guda biyu, Ministoci biyu suke dashi a gurare masu tasiri, kuma suna nan suna ta aikin gina mutanensu ‘yan shi’ah
Wadanda suka sadaukar da rayuwarsu suka kafa Gwamnatin shugaba Buhari (da taimakon Allah) ba su ne yau ake ci da su ba a cikin gwamnatin, wannan shine jarrabawan da Allah Ya mana
Hakika mafi akasarin mutanen da suke jikin shugaba Muhammadu Buhari a yanzu da sun san wahalan kafa Gwamnati da ba suyi watsi da halin da muke ciki ba, tabbas da sun fadawa shugaba Buhari gaskiya, kuma da yayi amfani da ita kasancewarsa mai son gaskiya
Yaa Allah Ka bamu ikon cinye wannan jarrabawa Amin
Ga bidiyon nan kasa ku kalla.
https://youtu.be/jyCLhzlf_74

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button