ASUU ta janye yajin aikinta na tsawon wata tara a Najeriya
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta janye yajin aikinta wanda ya fara tun watan Maris ɗin shekarar 2020.
Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba da safe.
Shugaban ASUU na ƙasa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da hakan a yayin taron da suka yi a Abuja, inda ya yi ƙarin bayani kan yadda ƙungiyar ta cimma hakan.
ASUU ta bayyana cewa ta amince da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata ne shi ya sa ta amince da janyewa bayan tsawon wata tara.
An sha kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU kan batun janye wannan yajin aiki na sai Baba ta gani.
Ɗaliban Najeriya sun yi ta roƙon gwamnati a lokuta daban-daban a shafukan sada zumunta ta hanyar amfani da maudu’ai da dama duk don a janye yajin aikin su koma aji.
.
Me ASUU da gwamnati suka cimma?
Ministan Ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ne ya jagoranci taron a Abuja.
Sun cimma yarjejeniyar ne bayan da suka shafe sa’a takwas suna ganawar sirri don sasantawa kan matsalar.
ASUU ta shaida wa BBC cewa sun yi murna da yadda gwamnati ta bi da lamarin wajen yi musu sabon tayi ita kuma ta gana da mambobinta sannan suka mayar wa gwamnatin martani kan matsayarsu cikin sa’a 24.
Manyan batutuwan da suka mamaye ganawar su ne na neman gwamnati ta biya jami’o’i kuɗaɗen gyare-gyare a kuma biya malamai alawus-alawus ɗinsu, a cire tsarin biyansu albashi na IPPIS sannan a biya su albashinsu na watanni da suka bi.
Gwamnati ta sasanta da su kan biyansu naira biliyan 40 na alawus da naira biliyan 30 na gyare-gyaren jami’o’i.
kamar yadda Bbchausa na ruwaito,Sannan gwamnati ta amince ta yi gwajin fasaha kan tsarin yadda ake biyan malaman jami’o’i albashi wanda suke kai na UTAS.
Zuwa ranar Talatar da ta gabata 22 ga watan Disamb, gwamnati ta biya maaman albashinsu na wata biyu da kuma alawus-alawus ɗinsu na naira biliyan 40.
Abin da ya saura ayanzu shi ne kuɗaɗen gyare-gyaren jami’o’in.
Matakan da ASUU ke bi kafin janye yajin aiki
Kafin ASUU ta janye yajin aiki akwai matakan da take fara bi tukunna.
Shugaban ASUU na ƙasa Biodun Ogunyemi ya ce tawagar jami’an ƙungiyar da suke tattauna wa da gwamnati ba su da izinin janye yajin aikin.
Yadda abin yake shi ne idan suka je teburin sulhu kuma gwamnati ta yi musu tayi, sai sun koma ga mambobinsu na dukkan rassan ƙasar don su ji ta bakinsu, sannan sai su sake duba tayin su cimma tasu matsayar, daga nan sai tawagar da ke jagorantar sasantawar ta koma da nasu buƙatun a taro na gaba da gwamnati.
Haka za a yi ta bin tsarin gabatar da buƙatun har sai Kwamitin Amintattu na ASUU da ya haɗa da dukkan shugabbanin sun amince kan tayin da suka ga ya fi kwanta musu a rai da gwamnati ta gabatar.

Coronavirus: Cikas na gaba ga ɗaliban
A yanzu da ASUU ta janye wannan yajin aiki, wata babbar matsala da za ta zama cikas ga sake buɗe jami’o’in shi ne hauhawar da annobar cutar korona ke ƙara yi.