Kannywood

Ali Nuhu Ya Shirya Ƙayataccen Fim Wanda Za A Fara Haska Shi A Ƙasashen Turai Da Ma Ƙasar Amurka (Hotuna)

….Wannan ƙayataccen Fim mai suna (BANA BAKWAI) na fitaccen Jarumi Sarki Ali Nuhu za a fara haska shi a Fim House SINIMA Shoprite Zoo Road Kano a ranar 25 ga wannan wata na Disamba, 2020.
Fitaccen jarumin nan na masana’antar Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu, wanda ake yi wa kirari da (Sarki), ya yi fitar barden Guza ya shirya wani ƙayataccen Fim wanda ba a taɓa shirya irinsa ba a tarihim masana’antar Fina-Finai ta (Kannywood).
Fim ɗin mai suna (BANA BAKWAI), an yi amfani da fasaha da ƙwarewa gami da kayan aiki irin na zamani domin gamsar da mai ƙallo da kuma isar da saƙo cikin sauri da nasara. Bugu da ƙari, akwai fitattu, kuma ƙwararrun jarumai a cikin Fim ɗin.
Dokin karfe sun ruwaito cewa fim ɗin (BANA BAKWAI), Fim ne da Sarki Ali Nuhu ya shirya shi domin faɗakarwa da wa’azantarwa dangane da abubuwan da su ke haddasa fitina da tashin hankali wanda ke haifar da barazanar tsaro a duniya. Fim ɗin ya taɓo abubuwa da dama kamar: matsalar ƙyashi, hassada, zamba cikin aminci, maƙici da baƙin ciki gami da ƙiyayya, kamar misalin yadda abubuwa su ke faruwa a Nageriya.
An tsara fim ɗin akan yadda ake shigar da matasa cikin ƙungiyoyin ta’addanci da kwaɗaita musu cewa Jihadi za su yi su samu lada ranar gobe ƙiyama domin a ɗauki matakan magance matsalar. Sannan Fim ɗin ya tabo yadda hassada ta ke sanya mutane su ke yi wa jama’a masu daraja ko shugabanni da ƴan siyasa masu yin alkhairi ga mutane sharri su ɓata musu suna. Fim ɗin bai tsaya a nan ba domin kuwa ya taɓo batun yadda ake safarar miyagun ƙwayoyi domin raunata hankali da tunanin matasa. Daɗi da ƙari, Sarki Ali Nuhu ya nuna yadda ake watsi da yara marayu da marasa iyaye da yadda hakan ke zama illa ga Al’ummah Idan suka faɗa hannun miyagun mutane.
Haka zalika, Fim ɗin ya yi nuni akan yadda ake shiryawa ƴan jarida masu ƙoƙarin binciken ƙwaƙwaf da bin diddigi maƙirci da jefa su cikin ƙangin rayuwa. Fima ɗin ya nuna faɗakarwa da jan hankali ga masu mummunan hali cikin al’umma domin su faɗaka su gyara. Sannan kuma ya nuna yadda gaskiya da nagartar ɗan adam ta ke taimaka masa wajen samun nasara akan maƙiya duk da maƙicin da ake shirya masa.
 
 
 

 

Wannan ƙayataccen Fim mai suna (BANA BAKWAI) na fitaccen Jarumi Sarki Ali Nuhu za a fara haska shi a Fim House Sinima a ranar 25 ga wannan wata na Disamba, 2020 sannan kuma za a cigaba da haska shi a ƙasashe daban-daban na Afrika da ma Nahiyar Turai. Ka da ku sake a ba ku labari ku shirya tsaf domin fara kallon wannan ƙayataccen fin na Sarki Ali Nuhu wanda ya samar da shi domin ilimantarwa da nishaɗantarwa da faɗakarwa gami da wa’azantarwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button