Labarai

ALHAMDULILLAH ! An Dawo Da Rundunar DCP Abba Kyari Hanya Kaduna zuwa Abuja (Hotuna)

Ina mai cike da farin cikin sanar da ‘yan Arewa cewa an dawo da dakarun ‘yan sanda kwararru na rundinar DCP Abba Kyari wato IRT kan hanyar Kaduna zuwa Abuja domin su cigaba da yakar masu garkuwa da mutane
Ga nan jarumi ASP Abdurrahman Muhammad Ejily babban yaron Sarkin Yaki DCP Abba Kyari wanda muke masa lakabi da Bush To Bush Commander, DCP Abba Kyari ya bashi jagorancin sansanin IRT akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, gashi nan yau a bakin aiki don tabbatar da tsaro
 
 
Wannan karon DCP Abba Kyari ya dawo kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kayan aiki masu aminci, Insha Allahu masu ta’addanci akan hanyar su ma ba zasu zauna lafiya ba, za’a ga canji kwanan nan
 
 

Datti Assalafy ya kara da cewa,ba karamin kuskure aka tafka ba da aka janye dakarun IRT da STS da SARS daga kan hanya saboda tsagerun ENDSARS, amma ko a yanzu an fahimci illar hakan
Muna rokon Allah Ya kare mana DCP Abba Kyari da jama’arsa
Allah Ya tabbatar musu da cikakken nasara Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button