Labarai

Zulum ya roki matasa su shiga zama ƴan banga A Borno

Gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya roƙi matasan jihar su shiga aikin sa-kai domin taimakawa a kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.
Gwamna Zulum ya yi wannan kiran ne bayan kisan da wasu da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka yi wa manoma 43 a wani ƙauyen da ke kusa da garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito,gwamnan kuma ya yi wannan kiran e lokacin da je ta’aziya da jaje ga mutanen garin Zabarmari da lamarin ya faru.
Sojojin Najeriya sun kasa kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram a arewa maso gabas, inda aka kashe sama da mutum dubu goma.
A makon da ya gabata sojoji shida rahotanni suka ce an kashe a wani harin kwanton ɓauna a Borno.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button