Za Mu Fara Assasa Tsangayar Ilimin Likita A Aikin Ginin Jami’ar Assalam
Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce aikin gina jami’ar ASSALAM mallakar kungiyar zai fara da gina tsangayar ilimin likitanci don muhimmancin aikin likita, jami’an jinya da sauran ilimin sassan kiwon lafiya ga al’umma. Shugaban na magana ne a taro da shugabannin kungiyar na kasa da kwamitin aikin kafa jami’ar a masarautar Hadeja da ke jihar Jigawa.
Shugaban ya ce za a aza a kuma cigaba da gina cibiyoyin dukkan nau’o’in ilimi don jami’ar ta amsa sunan ta na jami’ar duniya. Shugaban ya kara da cewa asusun ba da gudunmawa na dukkan jama’a na bude kuma a na cigaba da taimakawa don gudanar aikin ba dare ba rana. Sheikh Bala Lau ya ce jama’a na kishirwar samun gagarumar jami’a don samun ilimi mai amfani a duniya da gobe kiyama.
Sanarwa daga sakataren soshiyal midiya : Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Nigeria ??