Yar Gata! Yadda Hadimin Shugaba Buhari Ya Hana a kama Rahama Sadau
WANI mai yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ayyukan musamman shi ne ya hana ‘yansanda su kama Rahama Sadau, wadda har yanzu ta na zaman ta a Abuja, inji mutumin da ya kai ta ƙara.
Haka kuma ya yi iƙirarin cewa akwai wani jami’in ‘yansanda a Abuja wanda shi ne ma ya hana a kama ta a tafi da ita Abuja.
Idan kun tuna, wani mutum ɗan gwagwarmaya mai suna Malam Muhammad Lawal Gusau ya kai koke ga Sufeto-Janar na ‘Yansandan Nijeriya, ya na iƙirarin cewa Rahama ta aikata saɓo a kan Annabi Muhammadu (SAW) kuma ya kamata a kama ta a gurfanar da ita a kotun Shari’ar Musulunci.
Shi kuma Sufeto-Janar ɗin ya ba Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna, Umar Muri, umarnin ya binciki al’amarin don kada ya jawo tarzoma.
Mujallar Fim ta fassara wannan umarnin da cewa a kama fitacciyar jarumar ta Kannywood da Nollywood a yi mata tambayayi, wanda hakan na iya sa a tsare ta da sunan ana bincike.
Kwamishina Umar Muri ya tura tawagar ‘yansanda zuwa Abuja inda Rahama ta tafi tare da ƙannen ta da mahaifiyar su domin a zo da su Kaduna.
Sai dai, kamar yadda mujallar ta ruwaito a ranar Asabar da ta gabata, wani babban jami’in ‘yansanda ya sa baki a lamarin, ya ce a bar Rahama ta kai kan ta wajen ‘yansanda maimakon a kama ta a tafi da ita wanda kamar tozartawa ce a gare ta.
Mujallar Fim ta ruwaito wata majiya mai tushe ta faɗa mata cewa jarumar ta kama hanyar Kaduna inda ake jiran isar ta hedikwatar ‘yansanda wajen ƙarfe 4 na yamma.
To ashe da saura baya, inji masu iya magana. Ashe Rahama dai ba ta je Kadunar ba, ta ci gaba da zama abin ta tare da mahaifiyar ta da ƙannen ta mata su uku a wani ɓoyayyen otal a garin na Abuja, yayin da ‘yansandan da aka tura su zo da ita sun kasa taɓuka komai. Tilas su ka juya su ka koma gida.
A yau Litinin kuma sai ga zungureriyar wasiƙa zuwa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga Lawal Gusau inda mai ƙarar jarumar ya fallasa cewa wasu manyan mutane a fadar shugaban ƙasar sun shiga kes ɗin na Rahama dumu-dumu, sun hana a kama ta.
A buɗaɗɗiyar wasiƙar tasa wadda ya tura wa mujallar Fim, Malam Lawal, wanda ke zauna a gida mai lamba
Plot 83, Dutsi Sangwari Layout,
Ayo Salami Street, Abuja, ya yi wa Shugaba Buhari bayanai kamar haka:
“Assalamu alaikum, Mai Girma Shugaban Ƙasa.
Allah shi ƙara ma Mai Girma Shugaban Ƙasa lafiya, mai jin tausayin talakawa wanda su ka jajirce wajen tabbatar da cewa ka ci zaɓe saboda gaskiyar ka, tsoron Allah da kuma imani da kai cewa don saboda da yaƙinin su na cewa kai kaɗai ne za ka ceci talakawan Nijeriya daga ƙuncin da su ke ciki. Kuma har yanzu su na masu matuƙar ƙaunar ka a matsayin ka na Shugaban Ƙasar Nijeriya.
“Ya Mai Girma Shugaban Ƙasa, al’ummar Musulman duniya su na roƙon arziki a wajen ka domin ka tsawata, kuma ka sa baki a kan wani daga cikin jami’an gwamnatin ka da ya ke a cikin fadar ka, wanda ka ɗauki amana ka ba shi. Amma ya ci amanar ka bisa ga dalilin cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW), Fiyayyen Mahalicci, zuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda Allah ya halicci duniya da lahira da abin da ke cikin su saboda shi.
“Duk wani bani’adama ya na cin arzikin Manzon Allah (SAW).
“Mai Girma Shugaba, babban tuni, mun gabatar da takardar mu na koke ga shugaban hukumar ‘yansanda na Najeriya bisa ga yanda doka ta tanada a ranar Talata 3/11/2020, kuma ba tare da ɓata lokaci ba, shi shugaban hukumar ‘yansandan Najeriya ya bada umurni a rubuce zuwa ga kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kaduna (CP U.M. Muri) cewa a kamo Rahama Sadau.
“A nan take CP na Jihar Kaduna, bayan samun umurnin IGP na Nijeriya a dokance, a daren, CP na Jihar Kaduna ya umurci mutanen sa da su je a kawo mai Rahama Sadau. Kuma da isar mutanen sa Abuja tun ranar 4/11/2020, bayan aikin su na sirri, sai su ka gano inda aka ɓoye Rahama Sadau.
“Abin baƙin ciki, takaici da kuma ƙona zuciya, bayan ‘yansanda sun ritsa ta a otal a cikin birnin Abuja, sai Rahama Sadau ta ɗauki waya ta kira wani, kuma a nan take sai wanda ta kira ya zo.
“A nan take, wanda ta kira sai ya soma tambayan su ko su su waye? Sai jami’an ‘yansanda su ka nuna masu cewa su jami’an tsaro ne daga Jihar Kaduna.
“Daga bisani, jami’an tsaron daga Jihar Kaduna su ka faɗa ma wanda Rahama Sadau ta kira, kuma a nan take su ka nuna masa shaida cewa duk sun bi ƙa’idodi da doka ta tsara.
“Sai shi ya ce ma jami’an tsaron sun yi sa’a. Amma sai ya ce masu su fice su bar wurin nan, a gaban Rahama Sadau.
“Bisa ga bin doka da oda ta ɓangaren jami’an tsaron, jami’an tsaron sun yi niyyar cire kakin su domin yin faɗa a sanadiyyar cin mutuncin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (SAW) don duniya ta sani, wanda a bisani, su jami’an su ka canza shawara.
“A dalilin haka, su ka sanar da Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kaduna, inda ya sake umurtar su da su kasance masu bin doka da oda, wanda a kullu-yaumin, Mai Girma Shugaban Ƙasa ya ke umurta da su kasance masu bin doka da oda.
“A ranar 5/11/2020 (Thursday), Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna ya yi rangadi zuwa ga masallatai na Jihar Kaduna ɗaya bayan ɗaya don kada Musulmai su tada hankulan su a kan wannan iftila’i da Musulmai su ka samu kan su a ciki na ɓatanci game da Manzon Allah (SAW) dalilin hotunan Rahama Sadau. Kuma ya sake jaddada masu da roƙo cewa da su ci gaba da yi ma al’ummar Musulami nasiha kuma su kasance masu bin doka da oda kuma kar su yanke hukunci da kan su.
“Manya-manyan malamai na Jihar Kaduna sun taimaka ƙwarai da gaske a inda su ka sanar da Majalisar Ƙoli ta Harkar Addinin Musulunci wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ke jagoranta cewa kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kaduna ya ba su girman su, a inda su kuma su ka sanar da Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci tabbacin cewa ba za su sa maganar Rahama Sadau ba a huɗubar su bisa ga bayani da roƙo na mai girma kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kaduna. Allah ya saka mashi da alkhairi da wannan ƙoƙarin da ya yi, domin an sami zaman lafiya.
“A taƙaice, Mai Girma Shugaban Ƙasa, a lokacin da jami’an tsaro wanda kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kaduna ya turo su zuwa Abuja don kama ta, sun tarar da ita da mahaifiyar ta da kuma ƙannen ta uku mata da kuma wasu ƙawayen ta, ta na shirin zuwa filin jirgin sama na Abuja don gudu zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (U.A.E.). A wannan lokacin, wani jami’i mai muƙamin Kwamishinan ‘Yansanda, ya ci amanan alƙawarin da ya ɗauka, watau ‘Oath of Allegiance’, domin ya kama ta ya mara ma jami’an ‘yansandan baya don kawo ta zuwa Jihar Kaduna.
“Haka jami’an nan na ‘yansanda su ka dawo Kaduna ba tare da Rahama Sadau ba.
“Shi wannan jami’in ya ba su tabbacin cewa za ta kawo kan ta Kaduna ranar Asabar (7/11/2020), amma har yau Litinin (9/11/2020), wannan jami’i bai kawo ta ba, ita kuma ba ta kawo kan ta ba.
“Abin mamaki, wani daga cikin fadar Mai Girma Shugaban Ƙasa, wanda ya ke riƙe da wani matsayi wanda Shugaban Ƙasa ya ba shi na amana, a yau Litinin (9/11/2020), ni Lawal Muhammad Gusau na je Shelkwatar Rundunar ‘Yansanda na Jihar Kaduna tare da al’ummar Musulmai don mu ji ko ta iso? Sai DC CID, a ofishin CP, ‘Yansandan Jihar Kaduna, ya tambaye ni cewa ba ni ka kira ba da misalin ƙarfe 5:48 na yamma? Sai kuma wani jami’i mai muƙamin Sufeto (Inspr. Usman) wanda shi ne Shugaban Runduna, wato ‘Team Leader’, ya ce ma DC CID cewa Rahama Sadau DC CID ya kira.
“Sai DC CID ya riƙe hannu na ya shigar da ni cikin ofishin CP, Jihar Kaduna. Sai na ce ma CP cewa mun zo a kan koken mu dangane da Rahama Sadau da kuma sauran al’ummar Musulmi, a inda CP ya ba mu haƙuri kuma da cewa ya fi kowa damuwa a kan wannan magana don da ita ya ke kwana kuma da ita ya ke tashi.
“Ya ba mu tabbaci da a sanar da al’ummar Musulmi cewa ba da daɗewa ba Rahama Sadau za ta shiga hannu don duk duniya na sane da abin da ke tafe bisa ga wannan ɓatanci da aka yi ma Mafificin Halitta, Annabi Muhammad (SAW), don munafukai na ma Shugaban Ƙasa zagon ƙasa.
“Har ila yau, mu na ma mai girma Shugaban Ƙasa tuni a kan asarar da aka tabka a sanadiyyar zanga-zangar kawo ƙarshen SARS (Endsars), don a a yanzu haka, an kai Musulmai a bango.
“Mu na kira ga ya Mai Girma da ya ƙara sa baki kuma ka ƙara kira ga munafukan addinin Musulunci, maƙiya Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW), ɗaya na da muƙamin Kwamishina a Rundunar ‘Yansandan Najeriya kuma ɗaya na cikin Fadar Shugaban Ƙasa.
“Ita Rahama, in ta shigo hannun Hukumar ‘Yansanda, za su tabbatar da abin da mu ka faɗa, domin a cikin gidan mu ka samu bayanan sirri daga su jami’an ‘yansanda wanda CP na Jihar Kaduna ya turo zuwa Abuja don a zo mai da Rahama Sadau.
“Su jami’an ‘yansanda, bayan dawowan su daga Abuja, bisa ga umurnin CP na Jihar Kaduna, sun yi kuka da kuma nuna nadama a kan tozarcin da aka nuna masu kamar su ba jami’an tsaro ba.
“A ƙarshe, mu na isar da matuƙar godiya ta musamman ga shugaban ‘yansandan Jihar Kaduna a kan tsayin dakan da ya yi na cewa zai yi aiki tsakanin shi da Allah. Allah ya ƙara yi mashi jagora, ya kuma kare shi daga dukkan sharrin munafukan addini, musamman na Abuja wanda su ke taka rawa wajen hana zuwan Rahama Sadau.
“Manzon Allah (SAW) ya fi kowane Mahalicci daraja kuma Allah Maɗaukakin Sarki ba ya barin duk wanda ya taɓa Manzon Allah (SAW).
“Allah ya ƙara wa Fiyayyen Halitta daraja da ɗaukaka.
“Allah ya ƙara ma Shugaban Ƙasa lafiya da fatan ya kammala nauyin da Allah ya ɗora masa lafiya.
“Allah ya ba mu zama lafiya a babbar ƙasar mu Najeriya, amin.”
Daga waɗannan bayanan, mujallar Fim ta hango cewa Rahama Sadau dai ba za ta kamu ba, musamman bisa ga koken da Lawal Gusau ya yi game da ita, domin manyan da ta sani sun shiga cikin al’amarin.
Da ma Hausawa sun ce yaro da gari, abokin tafiyar manya!
Majiyarmu ta dauko wannam rahoto daga mujallar fim.
Allah ya tsine mata ya tozarta ta yasaka jahannama ne makomanta