Labarai
Yanzu – Yanzu : Wani Ya Rataye Kansa Har Lahira A Kano
Advertisment
Wani magidanci mai suna Ibrahim Abubakar da ke sana’a a titin gidan Zoo ya rataye kansa.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, kuma kafin a kawo masa ɗauki har ya rasa ransa.
Ɗan marigayin mai suna Abdussalam Ibrahim ya shaida wa Freedom Radio cewa, tare suka yi sallar la’asar da mahaifin.
Amma yana komawa shagon sai ya tarar ya rataye kansa.
Freedom radio ne na ruwaito labarin a cewar Abdussalam ya ce, “Mahaifin nasa yana fama da lalurar ƙwaƙwalwa, sannan yana cikin halin rashi ga shi kuma auren ƴarsa ya matso”.
Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce, zai bincika lamarin.
Allah ya kyauta gaba ya kuma karemu
Amen