Kannywood
Yanzu – Yanzu : An saki Sarkin Waka Nazir M Ahmad
Kotun Majistre da ke No-man’s-land ta saki fitacce mawakin nan Naziru Sarkin Waka, bayan ya shafe kwanaki biyu a tsare.
Lauyan mawakin, Barista Sadik Sabo Kurawa, ya shaidawa Freedom radio cewa, wanda ake tuhumar be aikata laifin da ake zarginsa ba.
Kotun dai na tuhumar mawakin ne, bisa zargin sakin wasu wakoki ba tare da sahalewar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kotun ta sake shi ne, bayan ya cika sharuddan da aka gindaya masa.
Karin bayyani na nan zuwa ku kasance da Hausaloaded.com
Madogara : freedom radio