Labarai

Tsohon gwamnan Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna da ke Najeriya Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu.
Ya rasu ne a birnin Kaduna yana da shekara 84 a duniya.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ya tabbatar wa BBC da wannan labari.
Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa – wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar ta Kaduna – ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.
Marigayin na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokradiyya.
 
 
Ya zama gwamna ne 1979 a karkashin jam’iyyar PRP, ko da yake an tsige shi kafin ya kammala wa’adinsa.
Daya daga ‘ya’yan jam’iyyar PRP, Sanata Shehu Sani, wanda ya tsaya takarar dan majalidar dattawan Najeriya a jam’iyyar a shekarar 2019, ya bayyana alhinisa bisa rasuwar tsohon gwamna.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button