Kannywood

Ran Maza Ya Ɓace ! Ali Nuhu Ya Murza Gashin Baki Game Da Matsalar Tsaron Arewa

Advertisment

Babban darakta Abdulmuminu tantiri byayi tsokani akan halin da muke ciki a Nigeria wanda anka yiwa yan uwanmu rankan rago a jahar borno wanda anyi dai dai duk ra’ayin ali nuhu hakane shima.
Ga yadda bayanin yake.
GWAMNONI:- Lokaci yayi da zaku wanke kanku a wajan alummar da kuke mulka,lallai idan har domin jama’a kukeyi to kuyi magana ku kuma dauki mataki mafi tsauri akan rashin tsaro a kasar nan.
SARAKUNA:- Har yanzu ku talakawa suke gani a matsayin iyayensu,kuma kunada daraja mafi girma a idanunsu fiye da yan siyasa,?Shin kuna tsoron ku rasa kujerunku ne fiye da ubangijinku?Idan babu talakawan wa zaku mulka,?ya kamata ku tabbatarwa da talakawanku kuna tare dasu,amanarsu da kare mutuncinsu.
SENATOCI/YAN MAJALISU:- Kun manata ne da cewa talakawa ne suka kaiku wadannan kujerun?Kun manta ne wakilcinsu kukeyi bisa amanarsu da suka damka muku?ko kun manta motocin da kuke shiga da offisoshin da kuke zaune da abincin da kukeji daga kudin talakawa ne?Lallai idan baku tashi tsaye ba akan wannan kashe kashe to wlh tun a duniya bazaku ga dai dai ba balle kuma a lahira.
ASUU:-Ance daga iyaye sai malamai,da ace yajin aikin da kukayi domin a shawo kan matsalar tsaro ce a kasar nan to da mutuncinku dana iyalanku ya samu karuwa a wajan alumma,Kunyi yajin aiki saboda kudi,yanzu kuma yaya za’ayi da kashe kashen da akeyi?ko anan baku da rawar takawa?
LABOUR:- Koda yake naga ku ma’aikata kunfi daukar mataki akan karin kudin mai ko kudin kayan abinci,to yaya kuma zubar da jini da tashin hankali da kidnapping yake a wajanku?Naga dai sai da rayuwa akecin abinci har a bukaci man fetir.Idan kunayi don jama’a to ku fito kuyi magana akan rayukan da ake rasawa a kasar nan.
Daga karshe ina kara rokon shugaban kasa da duk wanda yake rike da amanar talakawa da su kawo karshen wannan matsala take yanke.#securenorth #endinsecurity #stopkilling #rise&actnow”

 

View this post on Instagram

 

A post shared by ALl NUHU (@realalinuhu)

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button