Labarai

Na Rantse Da Girman Allah Matsalar Tsaron Arewa Ajanda Ce ~ Datti Assalafy

Advertisment

Ya ku ‘yan uwa ‘yan Arewa, bai kamata mu yiwa shugaba Buhari watsewar zabi ba, mu fahimci cewa idan ya gaza ta fannin tsaron Arewa bai gaza ta wani bangaren ba, kamar tallafawa matasa da kudi, ayyukan da suka shafi gina kasa da sauransu
Duk wanda ya bada gudunmawa aka zabi shugaba Buhari tun daga zaben 2015 da 2019 bai kamata ya guji shugaba Buhari ba a yanzu, masu karin magana sukace; “Hannunka ba zai rube ba ka yanke” magani zaka nema domin ka samu sauki, a yanzu Buhari taimakon masoyansa na gaskiya yake da bukata ko da kuwa addu’ah ne tunda ya tabbata gaskiya maciya amana sun gewayeshi, ga barazanan karnukan farautar yahudawa a kanshi
Buhari abin tausayi ne, akwai abinda yafi karfinsa, kunga wannan matsala na rashin tsaro a Arewa babu wani boye-boye yafi karfin Buhari, yafi karfin hukumomin tsaron Nigeria, domin ajanda ce aka tsara daga kasashen waje masu juya tsarin mulkin Demokaradiyyah, zan baku misali daya da NGOs da suka mamaye Borno suna cin amana, rundinar sojin Nigeria ta kama wasu NGOs din da hannu dumu-dumu suna taimakon Boko Haram ta dakatar dasu, amma babu dakatarwan da ta wuce awanni 24 wanda ba’a janye ba, saboda abin yafi karfin rundinar sojin
Me yasa sukace a rushe rundinar SARS a daidai lokacin da suke da amfani a Arewa?
Me yasa suka dakatar da rundinar DCP Abba Kyari na IRT da rundinar DCP Yusuf Kolo na STS wanda laifin SARS bai shafesu ba?, IRT da STS rundinoni ne guda biyu wanda babu irinsu a duk fadin nahiyar Afirka a bangaren kwarewa wajen yaki da masu garkuwa da mutane da bin diddiginsu, amma saboda laifin SARS sai aka hadesu aka dakatar da su? makirci ne da tuggu
Ba matsalace ta zaluncin ‘yan sandan SARS ba, ajanda ce daga turawa, zaku iya fahimtar hakan a daidai lokacin da tsagerun ENDSARS suke ta’addanci a Nigeria tare da cin amanar kasa; a daidai lokacin kuma manyan shugabannin turawa suke tsoratar da mahukuntan Nigeria game da daukar matakin dakile tsagerun ENDSARS din
Wallahi wasu bayanai na gaskiya da na samu, rahoto aka kaiwa lamba daya, kuma umarni ne cewa ba’a da bukatar rundina kaza, shikenan shi kuma lamba daya ba yadda ya iya sai yace a aiwatar don maslaha, na rantse da Allah matsalar tsaron Arewa ajanda ce ta musamman, da kuna ganin abinda muke gani muke ji muke samu na bayanan sirri akan tsaron Arewa watakila gashin kanku sai yayi furfura saboda tashin hankali
Munyi imani da Allah zalunci da makircin makirai ba abune da zai tabbata ba, Allah Zai kawo sauki, a dayan bangare kuma ya kamata muyi tunani, ta iya kasancewa akwai laifin da mutanen Arewa suka yiwa Allah Ya jarrabemu, sai mu gyara
Muna rokon Allah Ya kawo mana sauki da mafita na alheri ba don halin mu ba.
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button