Labarai

Matsalar Tsaro: Ba Laifin Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami Bane!

Shahararren marubucin nan Datti Assalafy yayi tsokaci akan yadda ake ganin laifin dr ali isah pantami akan Matsalar tsaro.
“An bar dukan jaki ana dukan taiki” abin takaici majalisar Dattawan Nigeria ta gayyaci Maigirma Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami domin su tuhumeshi akan matsalar tsaro da yake faruwa a Nigeria
Majalisar dattawa ta mika takardar gayyata zuwa ga Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami kan cewa ya bayyana a gabanta yayi mata wasu bayanai game da tsaron Nigeria.
Majalisar dattawan tace tana bukatan Dr Pantami ya bayyana yayi mata bayani akan me yasa har yanzu ake iya amfani da layukan waya (SIM cards) ake tattaunawa da masu garkuwa da mutane, har a karbi kudin fansa, ta hanyar tattaunawa ta wayar.
Matsalar garkuwa da mutane ba laifin Ma’aikatar sadarwa bane, wannan yana nuna mana cewa wakilan Nigeria ba su ma san inda matsalar take ba balle su fahimci hanyar da zasu magance
Yau idan kidnappers suka kama mutum suka tafi dashi jeji ba su cika yin amfani da wayoyinsu wajen kiran ‘yan uwan wadanda suka kama ba, da lambar wayan wanda suka kama suke kira domin karban kudin fansa, ko da anyi tracking an gano location babu kayan aikin da jami’an tsaro zasu iya shiga jeji su kubutar da mutumin daga hannun masu garkuwa da shi
Sannan fa da zaran kidnappers ya kamata mutum to ya zama Sarki, dole a lallabashi ya fadi abinda ake so a biyashi, imba haka ba kashe mutumin zasuyi, don haka inda matsalar take shine ME YASA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKE SAMUN NASARAN KAMA MUTANE BA TARE DA AN DAKILE SU BA? bada kariya ga mutane ba aikin ma’aikatar sadarwa bane, aikin hukumomin tsaro ne
Wallahi Tallahi Billahi matsalolin tsaron Nigeria ya ta’allaka ne akan cewa har yanzu jami’an tsaron Nigeria basu da isassun kayan aiki irin na zamani da zasu tunkari ‘yan ta’adda da barayin daji, da matsalar yadda ake bada horo wa sabbin jami’an tsaro, da karancin albashin da ake biyansu, da karancin yawansu shine inda matsalar tsaron Nigeria ta samo asali
A batun horo, ana amfani ne da tsarin horarwa na lokacin da duniya take kwance lafiya, don haka akwai bukatar a sabunta shi ya dace da zamani, musamman akan yaki da garkuwa da mutane wanda yake sabon abune da ya shigo mana Arewan Nigeria, hakanan a bangaren jami’an tsaro masu ilmin fasaha kamar Forensic, Tracking, Hacking da sauransu babu horarru da yawa, ya kamata ace a kowace karamar hukuma da jiha akwai Data Base Collection Centre wanda jami’an tsaro suke lura da harkan sadarwan barayi da ‘yan ta’adda
A batun kayan aiki, ita kanta bindigar AK47 da jami’an tsaron Nigeria suke rikewa tsohuwar yayi ce, gata da nauyi, sannan basu da isassun motoci, basu da kayan sakawa na sulke wanda harsashi bai iya hudawa, basu da isassun motoci masu sulke wanda zasu shiga jeji dasu don tunkarar barayi da ‘yan ta’adda, alhali Nigeria tana da karfin arziki da zata iya wadata jami’an tsaro da wadannan kayan aiki
A batun yawan jami’an tsaro, Nigeria tana da yawan mutane wanda sun haura miliyon 200, idan aka hade yawan jami’an tsaron Nigeria gaba dayansu daga kan Police, Soja, DSS, Civil Defence har da ‘yan banga da sauransu ba su kai miliyon 2 ba, wanda a ka’idar International Standard ana so a yawan mutane 10 a samu jami’in tsaro guda 1 a tare da su yana lura da sha’anin tsaro da neman bayanan sirri, don haka akwai matsala ta wannan fannin
A batun biyan albashi, ana biyan kurtun ‘dan sanda Naira dubu 45 a wata, wannan bai kai ya iya ciyar dashi abinci shi kadai ba, balle na iyalansa, kudin makaranta, kudin magani da sauran bukatu, kuma bai da wani lokacin neman sana’ai sai aikinsa, yaya zaiyi ya iya sadaukar da rayuwarsa da wannan albashin?
Don haka wadannan matsaloli ne da Majalisar Dattawa ya kamata tayi duba a kansu ta magance, domin iya abinda ma’aikatar sadarwa zata iya yi a fannin tsaro shine gano bayanan sirrin barawo ko ‘dan ta’adda wadanda suke amfani da kafofin sadarwa da kiran waya, idan an ganoshi yana boye a jeji aikin jami’an tsaro ne suje inda yake a jeji su yake shi
Zan bada misali da wata Software wanda ‘yan Boko Haram suke amfani dashi wajen yada sako a tsakaninsu, suna kiran Software din da suna “Asrarul Mujahideen”, zasu dauki bidiyo ko hoto su tura ma wakilansu ‘yan jarida, ko da sunyi amfani da service na Nigeria wajen tura sakon ba za’a iya tracking a gano ba
Datti Assalafy ya kara da cewa,Idan tracking jami’an tsaro suka yi sai ya nuna musu sakon na Boko Haram an turashi ne ma daga wata kasar ba Nigeria ba, alhali a Nigeria suka tura, idan Fixel Analysis jami’an tsaro suke nema akan bidiyo na Boko Haram, sai sun narkan bidiyon ya dawo asalin yadda aka daukeshi, saboda Software din da ‘yan ta’addan sukayi amfani dashi wajen daura bidiyon na sirri ne, amma duk da wannan akwai Software na miliyoyin Naira wanda idan gwamnatin Nigeria ta sayawa jami’an tsaro duk za’a iya ganowa
To amma da yake matsalolin tsaron na karewa ne akan talakawa, manyan masu iko da kasar basu damu da biyan bukatun jami’an tsaro ba, wadanda ya kamata su samar da mafita basa bin hanyoyin kasa balle kidnappers su kamasu jirgi suke hawa don haka ba zasu taba kulawa ba
Gareku masu girma Sanatocin Nigeria, matsalar tsaron Nigeria ba laifin ma’aikatar sadarwa bane, ga matsaloli can a sama su ya kamata a magance, ina tuna lokacin da Dr Pantami yake matsayin Darakta Janar a hukumar NITDA Nigeria lokacin da ake tsakiyar yaki da Boko Haram, babu network, shi ya tsarawa sojojin sama da kasa wata fasaha da zasu dinga musayar bayanai a tsakaninsu, fasahace da ta taimaka wajen yaki da Boko Haram a lokacin
Allah Ka bamu shugabanni na gari, Ka tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button