Sports

Matan Saudiyya zasu fara Talla Leda A wasan kwallon Ƙafa A Karon Farko

An fara gasar kwallon kafa ta mata a karon farko a Saudiyya, wadda aka dakatar a baya saboda bullar cutar korona.
‘Yan wasa mata sama da 600 da ya kunshi kungiyoyi 24 ne ke fafatawa a wasannin daga birnin Riyadh da Jeddah da kuma Damman don fitar da kungiyar da za ta lashe kofin bana.
Ranar Talata aka yi bikin bude gasar da yammaci, amma ba a nuna wasannin a talabijin ba, sai dai gwamnatin Saudiyya ta albarkaci gasar da cewar an dauko hanyar da mata za a dama da su a wasanni.
kamar yadda bbchausa na ruwaito,a shekarar 2018 aka amince mata a karon farko su shiga filin wasan domin kallon wasannin tamaula a kasar.
Tun a shekarun baya mahukunta sun hana mata shiga wasanni kamar yadda addini ya yi hani da al’ada, sai dai kuma wasu malamai masu ra’ayin rikau sun ce barin mata su shiga sabgar wasanni zai haifar da rashin tarbiya.
Wasa bakwai aka kara ranar da aka yi bikin bude wasannin a Riyadh da kuma Jeddah a gasar kwallon kafa ta mata a karon farko da ya kamata a fara tun cikin watan Maris.
Cikin sakamakon wasannin Tigers ta doke Jeddah Challenges 11-0 da wanda Al Riyadh ta casa Najd Al Riyadh da ci 10-1.
Kungiyoyin za su ci gaba da karawa a biranensu daga baya a fitar da wadanda za su kece raini don lashe kofin bana a karon farko.
Duk kungiyar da ta zama gwarzuwa za ta lashe kudin saudi Arabia wato Riyal 500,000 daidai da Dalar Amurka 133,000 ko kuma Fam 100,000.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button