Kannywood

Mai ƙarar Rahama Sadau ya haƙura

MUTUMIN nan wanda ya cinna wa Rahama Sadau ‘yansanda, Malam Muhammad Lawal Gusa, ya janye ƙarar da ya shigar a kan fitacciyar jarumar Rahama Sadau a kan ɓatanci da ya ce ta janyo ga Annabi (S.A.W.) saboda wasu hotuna da ta wallafa a soshiyal midiya.
Idan kun tuna, ƙarar da ya kai ta sa Sufeto-Janar na ‘yansanda ya umarci kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kaduna ya bincike ta.
Hakan ta sa kwamishinan ya tura jami’an ‘yansanda zuwa Abuja inda Rahama ta je tare da mahaifiyar ta da ƙannen ta mata domin su kamo ta, amma kuma hakan ba ta yiwu ba saboda wasu manya sun sa baki a lamarin.
A takardar tasa, mutumin ya bayyana janye ƙarar ne a cikin wata takarda da aike wa Sufeto-Janar da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna, inda ya ce hakan ya biyo bayan matsayar da manyan malamai su ka ɗauka dangane da lamarin.
Bugu da ƙari, Lawal Gusau ya aika da takardar zuwa ga wasu manyan malamai, waɗanda su ka haɗa da limaman wasu masallatai a Kaduna, wato masallacin Sultan Bello, Sheikh Khalid Sulaiman, da na masallacin Al-Mannar, Sheikh Muhammad Tukur Adam Abdullahi, da na masallacin Sheikh Ɗahiru Bauchi, Sheikh Abdulƙadir Hashim Bindawa, da kuma Sheikh Halliru Maraya.
A takardar wadda ya ba mujallar Fim kwafe, mutumin mazaunin Abuja ya ce ya janye ƙarar ne saboda an samu fahimta da kuma nadamar da jarumar ta yi, inda ta sha alwashin cewa haka ba za ta ƙara faruwa ba da izinin Allah.
Malaman addini dai sun bayyana muhimmancin ba Rahama uziri, musamman ganin yadda ta nuna damuwa da kuma nadamar abin da ta aikata.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button