Labarai

Laifin Sanata Ali Ndume A Gurin Su ~ Datti Assalafy

An tura sanata Ali Ndume gidan yari a daidai lokacin da jama’ar Borno da yankin Arewa gabaki daya suke da bukatar wakilai marassa tsoro masu fadin gaskiya akan tabarbarewan tsaron Arewa irinsa
Laifin Sanata Ali Ndume shine ya kasa gabatar da Maina Waziri a kotu wanda ya karbi belinsa, yanzu kotu tana neman Maina Waziri bayanan, yaki zuwa yaci amanar Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume shine sanata mai lura da harkokin rundinar sojin Nigeria a majalisar Dattijai, Sanata ne mai fadin gaskiya, magana ta karshe da yayi kafin a kaishi gidan yari shine cewa gwamnati ta dena yadda da tsarin canza tunanin ‘yan Boko Haram, domin a yanzu tubabbun Boko Haram ne suke taimakawa ‘yan uwansu na jeji da bayanan sirri
Muna goyon bayan doka tayi aiki akan kowa, da haka ne za’a samu adalci da zaman lafiya, karban belin wanda ake tuhuma da laifi tare da kin gabatar dashi idan ana nemansa tabbas laifi ne, to amma abin takaici me yasa irin wannan hukunci baiyi tasiri ba akan Sanata Abaribe wanda ya karbi belin kasurgumin ‘dan ta’adda tsageri Nnamdi Kanu shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa Kasar Biafra (IPOB)?
Da Maina Waziri da Nnamdi Kanu waye laifinsa yafi girma?
Maina Waziri satar kudin fansho ake zarginsa da aikatawa, shi kuma Nnamdi Kanu ta’addanci ya aikata da kuma cin amanar kasa, Nnamdi Kanu ya aikata mafi munin laifi wanda har sai da gwamnatin Nigeria ta ayyana kungiyarsa ta IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci, Sanatan da ya karbi belinsa ya gagara gabatar dashi a gaban kotu, me yasa ba’a tusa keyar Sanatan zuwa gidan yari ba kamar yadda aka yiwa Ali Ndume?
Wannan rashin adalci ne, nuna wariyar yanki ne da kuma nuna banbancin addini, laifin Sanata Ali Ndume shine kasancewarsa mai fadin gaskiya akan tsaron Arewa musamman yaki da Boko Haram, sannan da kasancewarsa Musulmi ‘dan Arewa, sun turashi gidan yari, sun rufe bakinsa, sai suyi abinda suka ga dama nan da shekaru dubu idan sun isa
Yaa Allah Ka bawa Sanata Ali Ndume mafita na alheri
Yaa Allah Ka sa wannan abin ya zama sanadinn daukaka darajarshi a Nigeria Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button