Karya Ta ƙare ! Budurwa ta tsinke mazakutar mai fyade Bayan Ya Bukaci ta tsose Masa Ita
Wata Juanita, ‘yar kasar Ghana, ta ciza mazakutar wani Emmanuel bayan yayi mata fyade
Ya shiga dakinta tsakiyar dare da bindiga, inda ya kwashe mata duk wasu kayan alatu sannan yayi mata fyade
Duk da haka bai gamsu ba, sai ya nemi ta tsotsi mazakutarsa, take a nan ta guntule ta da hakora
Juanita, wata ‘yar kasar Ghana mai shekaru 24, ta guntule mazakutar Emmanuel Ankron, wani dan fashi da ya nemi ta tsotsi mazakutarsa da karfi da yaji.
Wasu maza suna samun kololuwar jindadi da lagwada idan mace ta tsotsi mazakutarsu. Emmanuel ya so ya mori wannan dadin daga budurwar.
Kamar yadda BBC ta ruwaito, lamarin ya faru ne a wuraren Obuasu dake bangaren Ashanti a kasar Ghana ranar Asabar.
Ankron, dan shekara 23 ya shiga dakin Juanita da tsakar dare da addarsa da bindigar toka. Bayan kwashe kudadenta, talabijin da wayarta, yayi mata fyade.
Duk da hakan yaji bai gama gansuwa ba, sai ya bukaci ta tsotsi mazakutarsa kafin ya bar dakin.
Kamar yadda Juanita ta sanar wa ‘yan sanda, ta ciza mazakutarsa har tayi nasarar guntuleta.
“Mutumin ya umarceni da in tsotsi al’aurarsa, ban yi kasa a guiwa ba na datseta da hakora,” a cewarta.
Mai fyaden ya yi hanzarin lallabawa ya bar dakin, saboda tsananin azaba da jinin da yayi ta zuba.
Budurwar, wacce daliba ce ta yi gaggawar tafiya asibiti don a duba lafiyarta.
Bayan ta isa asibitin ne tayi arangama da wanda yayi mata fyaden, ya je ganin likita, sai tayi gaggawar kiran ‘yan sanda inda suka tafi dashi.
Godwin Ahianyo, kakakin ‘yan sandan bangaren Ashanti, ya ce an gama bincike tsaf a kan al’amarin. ‘Yan sandan sun ce sun adana ragowar mazakutar mutumin a asibiti don saukaka bincike.majiyarmu ta samu wannan kabari daga Legit.