Karshen Faransa 3: Batanci Ga Annabi !Asarar Da Kasar Faransa Ta Fara Shiga ~ Dr. Prof Mansur Sokoto
– A cikin satin nan wasu manyan yan kasuwa guda uku daga kasashen Gulf sun yi transfer na kudi zunzurutu har Dalar Amurka biliyan shida ($6,000,000,000.00) daga bankunan Faransa zuwa wasu bankunan na kasashen Swiss da Belgium
– Kasar Pakistan ta soke kwangilar wasu kananan jiragen da ta kulla da kasar Faransa wadanda kimar kudinsu ta kai Dalar Amurka miliyan dubu daya da miliyan dari takwas ($1,800,000,000.00)
– Fitaccen dan kasuwar nan dan kasar Saudia Ahmad Áli Yazin ya soke kwangilar sayen motoci Peugeout guda 2800 kirar kasar Faransa wadanda kudinsu ya kai Dalar Amurka miliyan dari biyu da hamsin ($250,000,000.00).
– Kasar Turkey ta soke kwangilar da ta ba wa kasar Faransa ta kera makaman harbo jiragen sama wadanda kimarsu ta kai Dalar Amirka miliyan dubu daya da miliyan dari biyu ($1,200,000,000.00).
– An ga ma’aikatan manyan shagunan Carfour mallakar Faransa da suke birjik a kasashen Gulf da Morocco suna ta hamma saboda babu masu zuwa sayen kayansu.
– Ma’aikatan wani babban dilan kayan Cosmetics na Faransa da ke Kuwait sun share kwanaki biyu suna loda ma motocin shara kayayyaki mallakar kamfanin ana konawa.
– A yan kwanakin nan cutar Corona ta addabi muranen kasar Faransa.
Farawa kenan..
Ga yadda zaka gane kayan kasar Faransa daga lambarsu.. suna farawa ne da: 33…