Labarai
Innalillahi ! Daga Yau Karku Sake Alaƙantani Da Addinin Islama ~ Muneerat AbdulSallam
Shahararriyar karuwar nan Mai suna muneerat Abdulsalam ta rubuta a shafinta na Facebook tana cewa Daga yau bana fatan a sake alakanta Ni da musulinci, tsawon shekaru 2 da suka gabata na sake karbar addinin musulinci ban sami komai ba banda barazanar mutuwa, zagi, kiran suna, ba su taba yarda da gaske ko nuna min wani irin soyayya ba, a matsayin marainiya kuma yarinya da ta daga kanta a cikin wannan mawuyacin halin.
Abin da kawai nake so shi ne in ji na cancanta da karbuwa, amma hakan ba zai taba faruwa ba kuma na gaji, imani na ya kasance tare da Allah Madaukakin Sarki kuma hakane, dukkanku kuna iya kashe ni yanzu idan kuna so, amma na isa wannan gidan wuta a duniya.
Allah ya shiryaki