Labarai

Innalillahi : Allah Yayiwa Ali Kwara Rasuwa

Allah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar fitaccen Mafarauci ‘dan baiwa Alhaji Aliyu Muhammad wanda yafi shahara da ALI KWARA yau juma’a a wani Asibiti dake birnin Tarayya Abuja
Ali Kwara mutumin garin Azare karamar hukumar Katagum jihar Bauchi, ya shafe shekaru kusan 35 yana fada da manyan barayi ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane a fadin jihohin Arewan Nigeria
daga Datti Assalafy,ali Kware shiryayyen Mafarauci ‘dan baiwa, yayi fada sosai da manyan barayi, yana yawan fadin cewa watarana barayi su zasuyi ajalinsa, amma cikin ikon Allah duk tsananin yaki ba su taba samun nasara a kanshi ba, hakika ya taimaki tsaron Nigeria ta fuskoki da dama
A sanina sau daya ne harsashin bindiga ya taba shiga jikin Ali Kwara wani lokaci da ya shiga jeji farauta ya rungumi wani Gwanki zai kamashi, sai ya umarci daya daga cikin yaransa ya harbi gwankin saboda gwankin yana neman ya rinjayeshi, a dalilin hakane sai bullet ya tabashi, wanda har sai da ya fita kasar waje jinya
Allahu Akbar maza an kwanta dama, wannan babban rashi ne wa Nigeria gabaki daya, amma Alhamdulillah ya bar baya da alheri, kuma ya bar magaji, akwai daya daga cikin yaronsa na jikinsa da ya gaji baiwa irin nasa, idan ban manta ba ana mishi lakabi da Balbata
Na yiwa Ali Kwara farin sani, babu inda ban sani ba a gidansa dake Azare wanda muke yiwa gidan lakabi da lahirar ‘yan fashi, akwai ankwa da ake garkame barayi a gidansa yafi dubu
Rayuwa kenan, yau Ali Kwara ‘dan baiwa ya tafi ya barmu
Allah Ka yafe mishi laifukansa
Allah Ka kyautata makwancinsa
Allah Ka saka masa da Aljannah
Allah Ka kyautata karshenmu

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA