Uncategorized

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun amarya Nwakaego sun janyo masa caccaka

Dan gwamnan Jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya sake fitar da wasu sabbin hotunansa tare da matar da zai aura mai suna Halima Nwakaego Kazaure.
Bello ya wallafa hotunan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata 17 ga watan Nuwamban 2020.
Hotunan sun nuna Bello tare da Nwakaego a wani wuri mai kyau tare da furanni a bayansu sun kuma riko juna.
 
Irin wannan yanayin da suka dauki hotunan ya janyo cece-kuce musamman a shafin Twitter inda wasu da dama suka janyo hankalin Bello cewa abinda ya yi ya saba wa koyarwar addinin musulunci har ma da al’addar bahaushe dan arewa.
Ko a kwanakin baya ma Bello El-Rufai ya fitar da wasu hotunan biyu tare da suka dauka tare da sahibarsa Halima Nwakaego.
Wasu mutanen kuma suna ganin bai dace a tsaya ana bata lokaci a kan hotunan da ya wallafa a a yayin da matsaloli irin na tsaro da sauransu na addabar mutane.
 
Ga dai wasu daga cikin ra’ayoyin mutane da suka yi tsokaci a shafin na Twitter.
@AbdulMalumfashi1 ya ce, “Kaji tsoron Allah Bashir. Wannan hoton bai dace dakaiba.
@oluwatosinodun2 ya ce, “Ina takaicin yadda aka hada ni kasa daya tare da irinku. A maimakon ku mayar da hankali kan yi wa shugabanni magana game da rashin tsaro kun fiye damuwa da abinda wani ke yi a rayuwarsa. Duk abinda mutum ya ga daman bautawa matsalarsa ne.
@Kaneem7 ya ce, “A lokacin da @Rahma_sadau ta wallafa hotuna, kun yi ta mata fada amma yanzu babu wanda ke magana… Ina muku fatan alheri.
@BABANZAURE22 ya ce, “Fada alheri ko kayi shiru. Me yasa zaka yanke hukunci bayan Allah ne Alkalin Alkalai.
@soltan212 ya ce, “Saba dokokin Allah da Manzonsa ba zai haifar maka alheri a aurenka ba. Kana bukatar albaraka Allah a gidanka fiye da yabon da mutane za suyi maka. Ya Allah ka yi magana jagoranci @hadizel
Tattara wannnan bayyanai mun samu shine daga jaridar Legit.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button