Kannywood

Falalu Dorayi Yayi Martani Akan Kama Sarkin Waƙa Nazir M Ahmad Masu Daukar Hankali

A yau mun samu labarin babban darakta falalu dorayi yayi Martani da kalmai masu ma’ana akan rikicin da tsakanin nazir m ahmad sarkin waka wanda yana da kyau ayi amfani da wadannan nasiha.
Ga jawabin da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Siyasa mai wucewa ce, a kasar nan masu masu Manya laifi ma Afuwa ake musu, Yan boko haram, masu garguwa, barayin shanu, barayin dukiyar Al’umma mun gani an musu Afuwa .
Amma MUTUM da Yan uwansa yaki afuwa, yai ta jan magana, ana canja Kutu, kamar an kama su da laifin JUYIN MULKI.
Mulki jarabawa ce, kai fata ka kare lafiya babu hakkin wani akanka.
Duk Shugaba yana daukar darasi ne daga wanda suka gabace shi. In sunyi gaskiya yai irin aikin su, idan zalinci su kai ya zama ishara da irin makomar su.
Ga misali nan akan daya daga cikin Shugabannin da suka bar kujerar da ka hau. Akwai MISALAI.
Adalci shine in an sami laifi sanar da kungiya ta kawo maka Danta (wane), kungiya ko ta amshin shata ce tana da rana, domin sanadinta ka sami kujerar. Idan da kuna shawartar juna, kila kai da su zaku iya cimma mas’laha ba sai anje kotu ba.
Laifukan duk Mutum ukun nan da kuke kotu dasu, laifi ne da za’a iya zama a tebur a gama shi, Amma siyasa ta hana ai mas’laha, sai anyi tozarci.
Adawa ta kare akan KWANKWASIYYA da GANDUJIYYA, amma Sai gashi @govumarganduje na wishing kwankwaso BIRTHDAY. Wannan kadai ISHARA ce. Ka zauna da Yan uwanka lafiya, Idan ma umarni ne ake samu daga wasu, umarnin da zai bata zumunci da mutuncin juna barin sa yafi alkairi.
Abu ne mai kyau yin Jagoranci da mashawarta nagari, domin yana taimawa ai mulki da adalci. Mulki don bukatar wasu ba abin da zai haifar Sai son zuciya da zalinci.
Musani akwai ranar nadamar rashin adalci zata zo.
Mas’laha tafi GIYAR mulki, a koma teburin mas’laha tare da kungiya. Tunda kai Danta ne, duk suma ya’yan ta ne, kuma dama an kafa hukumar ne saboda Yan film.
Allah ya tsaremu baki daya, yasa a cinma matsaya mafi alkairi ga kowa. Amin.
domin mantuwa, muna tuni.
Ga dai fadin Allah.
Qurani a cikin An-Nisa’i (58)
Allahu (SWT) Yace;
“Lallai ne Allah yana umarnin ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.
KUMA IDAN ZAKU YI HUKUNCI TSAKANIN MUTANE, KUYI HUKUNCI DA ADALCI, LALLAI NE ALLAH MADALLA DA ABIN DA YAKE YI MUKU WA’AZI DA SHI.
LALLAI NE ALLAH YA KASANCE MAI JI NE, MAI GANI”.”







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button