DA DUMI-DUMI |Ta Tabbata EFCC Ta baza komar neman mutumin Nan Da Ya kirkiro INKSNATION A Najeriya (Hoto)
Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta baza komar ta tana neman Omotade-Sparks Amos Sewanu, wanda ya kirkiro tsarin nan na InksNation bisa zargin damfarar kudi naira Miliyan Talatin da Biyu (N32M) tare da yunkurin kirkiro wani sabon kudin zamani da ake kira “Pinkoin”.
A cikin wani labari da kamfanin jaridar The Nation ya wallafa a ranar Larabar nan, EFCC ta zargi Sewanu da mallakar makudan kudade ta hanyar karerayi da yaudara.
Sewanu dai ya dade yana ikirarin cewa zai kawar da talauci a fadin Najeriya cikin watanni 6 ta hanyar bawa kowani dan Najeriya kudi naira dubu Dari da Ashirin (N120,000) kowani wata a tsarin InksNation da ya fara gabatarwa tun a shekarar 2019.
A cikin wata takarda da ya rubutawa hukumar EFCC, Omotade-Sparks Amos Sewanu, ya bayyana cewa jariran da ake haihuwa kowacce rana ma zasu sami kudi naira dubu Dari da Ashirin (N120,000) a kowacce rana.
Ya kuma cigaba da rubutu a shafin InksNation na Tweeter, yana mai ikirarin cewa idan har wancan kudurin na sa na cirewa ‘yan Najeriya talauci bai sami nasara ba a cikin shekara daya, to a yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan Yari.
Yanzu haka dai hukumar EFCC na neman sa ruwa a jallo bisa damfarar makudan kudade da yayi.-Hausa7 Nig
Sai ku shiga wannan link domin tabbatar da wannan labari shiga https://efccnigeria.org/efcc/wanted