Kannywood

Bita da ƙulli ake yiwa Sarkin Waƙa – Aminu Saira

 
Dangin mawaƙi Nazir M. Ahmad sun ce akwai bita da ƙulli cikin ci gaban shari’arsa da hukumar tace finafinai ta Kano.
Ɗan uwan mawaƙin Malam Aminu Saira ya shaida wa Freedom Radio cewa suna zargin ana amfani da saɓanin da Naziru ke da shi da wasu wajen yi masa bita da ƙulli.
A ranar Laraba ne wata kotu a nan Kano ta soke belin da aka bai wa mawaƙin inda ta gindaya wasu sabbin sharuɗa.
Kotun ta tsare Nazirun tare da aike wa da shi gidan gyaran hali saboda rashin cika sharuɗan belin a kan lokaci.
Sai dai daga baya Nazirun ya cika sharuɗan amma an gaza samun alƙali ta wayar tarho a cewar Malam Aminu Saira.
Menene zargin da hukumar tace finafinan ke yiwa Nazir M. Ahmad?
Aminu Saira ya ce, hukumar na zargin Naziru da fitar da wasu kundin waƙoƙi a shekaru shida da suka wuce.
Ya ce, “Waƙoƙin da ake tuhumar sa, ba shi ne ya fitar ba, ƴan kasuwa ne kuma ba da sunan kamfaninsa ba, kuma an fitar da waƙoƙin tun zamanin mulkin tsohon gwamna Kwankwaso”.
Abin da Naziru ya faɗa a hanyar sa ta zuwa gidan gyaran hali
Yayin da ake kan hanyar tafiya da shi zuwa gidan gyaran hali ya ce ya miƙa wannan al’amarin ga Allah.
Ya ƙara da cewa “Wanda ya san manufata to wannan abu da ya faru ba zai sanya na bar inda na nufa ba” a cewarsa.
Me ƴan masana’antar Kannywood ke cewa?
Wasu cikin masu ruwa da tsaki a kan harkokin masana’antar finafinan Hausa na cewar, ya kamata hukumar ta tace finafinai ta riƙa hurawa kafin ta busa.
Hajiya Zainab Ahmad wadda aka fi sani da Bint Hijazi na cikin iyaye a masana’antar.
Ta shaida wa Freedom Radio cewa, ya kamata hukumar tace finafinai ta riƙa ajiye banbancin siyasa a gefe ta tabbatar da ta yiwa kowa adalci.
Ta ci gaba da cewa “Shugabannin nan su sani idan yau su ne, to gobe ba su ba ne, yau ina shugabannin da suka gaba ce su?”.
Me hukumar tace finafinai ta ce a kai?
Dangane da zargin cewa hukumar na yin bita da ƙulli ga mawaƙin, mun yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban hukumar Malam Isma’ila Na’Abba Afakallah.
Sai dai yayin da muke haɗa wannan rahoto, mun shafe kusan sa’o’i biyu muna kiran wayarsa amma bai ɗauki wayar ba.
Mun kuma aike masa da tagwayen saƙonnin kar-ta-kwana waɗanda har kawo wannan lokaci bamu samu amsa daga gareshi ba
Daga bisani mun ƙara kiran wayarsa inda aka ce yana tsaka da amsa wani kiran, mun yi ta gwadawa daga baya, ƙarshe kuma aka ce damu wayar a kashe ta ke.
Farkon kamun da aka yiwa mawaƙin
A watan Satumba na shekarar 2019 aka fara cafke mawaƙi Naziru M. Ahmad amma daga bisani kotu ta bayar da shi beli.
Bayan da ya cika sharuɗan biyan kuɗi har N500,000 da kuma tsayawar manyan ma’aikatan gwamnati guda biyu da mai unguwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button